Ƙamshi abin so ne a wurin kowa. Mata su kasance suna saka turaren wuta a kullum. Su mayar da shi dole kamar yin wanke-wanke.
Ko kun san cewa, wannan turaren wutar za a iya amfani da shi da kabbasa domin turara zanin gado da rigar sawa?
An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aikiBayan haka, akwai turaren humra wadda za a iya shafa shi a gashin kai.
Akwai na hammata daban sannan akwai na shafawa kamar mai, wanda aka fi sani da kulacca da kuma na riga.
Lallai duk macen da ta kasance cikin ƙamshi, za ta sami girmamamwa a cikin al’umma da kuma mai gidanta.
Kuma akwai turaren kanti kamar su ‘Dior’ da cool water da sauransu.
Yadda za ai amfani da turaren gargajiya
A sami kabbasa (za a iya saminsa a kasuwa) da kasko, a zuba garwashin wuta sannan a dora kabbasar a kai.
A kuma zuba turaren wuta a cikin garwashin sannan sai a rufe kabbasa da kayan da za a saka a ranar ko kuma wanda za a je unguwa da su, hayakin ya shiga kayan sosai.
Bayan haka, sai a shafa kulaccam (kamar man shafawa yake amma da turaruka aka hada shi).
Bayan an yi wanka sai a shafa a matsayin man shafawa. Sannan sai a saka riga a shafa humra fari ko baki a jikin kayan.
Idan kayan mai duhu ne sai a saka humra baƙa. Idan kuma kayan masu haske ne sai a saka farar humra.
Idan kuwa ana son amfani da turaren kanti, fesawa kawai ake yi.
Amma na gargajiya ya fi daɗewa a jiki don kuwa ko kaya sun yi datti da ƙyar a ji warin kayan don ƙamshin turaren.
Irin waɗannan turaruka na taimaka wa masu jego wajen rage ƙarnin nono a jikinsu da kuma jikin jariri.
Sai a ga wasu matan daga sun haihu, suna ƙarni, ɗan da suka haifa ma idan an ɗauka sai a ji cewa yana ƙarni.
Wani ƙarnin jinjirin ma har ya shafi wanda ya ɗauki jinjirin.
Don haka, sai a kula wajen amfani da turare domin magance waɗannan matsalolin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Turare
এছাড়াও পড়ুন:
An Fara Amfani Da Dandalin Samar Da Bayanai Na Kasar Sin
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp