HausaTv:
2025-03-04@19:21:37 GMT

Masu Alaka

Published: 4th, March 2025 GMT

Iran Tayi Tir Da Shirin Shugaban Amurka Na Sake Tsugunar Da Al’ummar Gaza

Kakakin gwamnatin kasar iran Fatime mohajerani ta yi tir da aniyar  shugaban Amurka Donald trumph na kwashe alummar gaza zuwa wasu  wurare, kuma ta biyyana shi a matsayin ci gaba da siyasar kisan kare dangi kan alumma falasdinu,

Shugaban na Amurka Donald trump yayi wannan bayanin ne a taron manema  labarai  da yayi a fadar white hause da fira ministan isra’ila binjamin natanyaho a watan jiya, inda ya nuna aniyarsa ta kwashe alumma yankin gasa zuwa wasu kasashen larabawa.

Tare da gina wajen shakatawa da babbar tashar jiragen ruwa a wajen.

Shuwagabannin  kasashen laraba wa da na musulmi sun jadda mastayinsu na amincewa da yancin falasdinawa tare da yin watsi da duk wani yunkuri na rabasu da gidajensu.

Wasu masharhanta na ganin shirin na Amurka zai jawo a mata mayar da ita saniyar ware a harkokin diplomasiya har ma tsakaninta da sauran kawayenta a yankin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tawagar ECOWAS Ta Fice Daga Guinea-Bissau Bayan Barazana Daga Shugaban Kasar

Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar.

A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.”

Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau tsakanin ranakun 21 zuwa 28 ga watan Fabrairu domin taimakawa wajen warware rikicin siyasar kasar dangane da sanya ranar gudanar da zaben shugaban kasa.

ECOWAS ta ce ta bar kasar ne don gujewa wannan wulakanci.

Kafin hakan dai shugaban kasar ya gana da tawagar ta masu shiga tsakani na kungiyar ta ECOWAS a ranar Litinin da ta gabata.

 Amma daga bisanio ya zarge su da wuce gona da iri ta hanyar tattaunawa da wasu shugabannin ‘yan adawa.

Ita dai tawagar ta ECOWAS, an dora mata alhakin samar da mafita ta samar da zaman lafiya a kasar Guinea-Bissau, ta hanyar mai da hankali kan cimma matsaya ta siyasa kafin zaben da aka shirya yi a ranar 30 ga watan Nuwamba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Umaro Sissoco Embalo ke shiga takun tsaka da tawagar ECOWAS a kasar sa ba. A lokacin da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa tare da goyon bayan jami’an tsaro, ya kori mambobin ECOWAS da ke kasar tare da tare da cewa bai maraba da wakilin kungiyar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Za Ta Kakaba Karin Harajin Kwastam Kan Wasu Kayayyakin Amurka
  • Trump Ya Dakatar Da Taimakon Da Kasarsa Take Bai Wa Ukiraniya
  • Tawagar ECOWAS Ta Fice Daga Guinea-Bissau Bayan Barazana Daga Shugaban Kasar
  • HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja
  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Gargadi Malaman Da Ba Sa Zuwa Aiki
  • Kasancewar Zaman Lafiya Na Dogon Lokaci Tsakanin Sin Da Amurka Abu Ne Da Ya Zama Wajibi
  • Kasashen Somaliya Da Habasha Suna Gab Da Rattaba Hannu Akan Amfani Da Tashar Jirgin Ruwa
  • Shugaban Kasar Ukraine Ya Sami Tarba Mai Kyau A Burtaniya Bayan Cacan Baki Mai Zafi Da Trump
  • Hamas Ta Bukaci Falasdinawa A Birnin Qudus Su Sabawa Dokar Takaita Yawan Masu Shiga Masallacin Al-Aksa A Kudus