Kasar Yamen Ta yi Alwashin Fadada Hare-hare Kan Israila Matukar Ta Dawo Da Kai Hari A Gaza.
Published: 4th, March 2025 GMT
Rahotanni sun nuna cewa kasar Yamen ta gargadi isra’ila game da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a gaza, kana ta yi alkawarin fadada hare-harenta a tel Avivi matukar ta dawo da kai hari kan alummar falasdinu,
Tace: matakin da isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin agaji da jin kai a yankin gaza, da kuma rufe dukkan mashigar dake isa zuwa yankin, take dukkan dokokin kasa da kasa ne da kuma yarjejeniyar da aka cimma.
Ana sa bangaren shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar yamen sayyid Abdul malik Hutsi ya bayyana cewa matukar Isra’ila ta dawo da kai hari a yankin Gaza to za ta mayar da martani mai tsananin a ko ina a Israila musamman birnin tel aviv.
Wannan sanarwar ta jawo damuwa sosai ga manyan jami’an tsaron Isra’ila , kuma sun dauki gargadin na Ansarullah da gaske domin zai jefa su cikin mawuyacin yanayi fiye da na baya a cewarsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila ta sake kai hare-hare ta sama kan kasar Siriya
Jiragen yakin Isra’ila sun kai karin hare-hare ta sama kan kasar Siriya, inda suka bijirewa gargadin Majalisar Dinkin Duniya game da hadassa asarar fararen hula yayin da suke ci gaba da kai wa kasar ta Larabawa hare-hare.
Rahotanni sun ce a ranar alhamis, jiragen saman Isra’ila sun kai hare-hare a kalla sau biyu a kan wuraren da sojoji a kusa da birnin Damascus, inda bayanai suka ce sun kai hari a yankunan Al-Kiswah da Al-Muqaylibah.
Kawo yanzu dai babu rahoton asarar rayuka.
Hare-haren sun zo ne kasa da kwana guda bayan hare-haren da Isra’ila ta kai makamancin haka inda ta kashe mutane 13.
Fararen hula 9 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata a wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai a lardin Dara’a da ke kudu maso yammacin kasar Siriya a yammacin ranar Laraba.
Isra’ila dai ta tsananta kai hare-hare kan Siriya tun bayan da ‘yan tawayen HTS suka karbe iko daga hannun gwamnatin Bashar Al’Assad a watan Disambar bara.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria Geir Pedersen a ranar Alhamis ya yi Allah wadai da karuwar hare-haren soji da gwamnatin Isra’ila ke yi, yana mai gargadin cewa suna yin zagon kasa ga yunkurin sake gina kasar Syria da kuma kara jefa kasar cikin mawuyacin hali.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce “Irin wadannan ayyuka na kawo cikas ga kokarin samar da sabuwar kasar Siriya mai zaman lafiya da yankin, da kuma jefa Siriya a cikin wani mawuyacin hali.”
Tun bayan rugujewar gwamnatin Bashar al-Assad, sojojin Isra’ila ke kai hare-hare ta sama a kan cibiyoyin da suke bayyanawa da na soji, da kuma rumbun adana kayan yaki na sojojin Siriya.