Aminiya:
2025-04-04@01:01:32 GMT

Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja

Published: 4th, March 2025 GMT

Ana fargabar cewa wasu masu ta’adar garkuwa da mutane sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), David Shikfu Parradang a Abuja.

Majiyoyi sun shaida wa ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya Zagazola Makama cewa ’yan ta’addan sun ɗauke Parradang a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar da safiyar wannan Talatar.

Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace

Makama ya ce ’yan ta’addan sun biyo sawun tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ne bayan ya ciro kuɗi a banki, inda suka karɓe kuɗin sannan kuma suka kashe shi.

Wannan lamari dai ya sake ɗaga hankalin mazauna Abuja a fannin tsaro musamman yadda a bayan nan ta’adar kashe-kashe da garkuwa da mutane ke ƙara ƙamari.

Parradang dai ya shafe fiye da shekaru 30 yana aiki a Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, inda ya riƙe muƙamai daban-daban a faɗin ƙasar cikin har da kujerar Kwanturola-Janar na ƙasa.

Ya yi aiki a jihohin Kano, Legas, Kwara, Enugu da Abuja, sannan ya yi kwasa-kwasai na neman ƙwarewa da sanin makamar aiki a nan cikin gida da ƙetare.

Tuni hukumomin tsaro suka soma gudanar da bincike domin bankaɗo masu hannu a wannan aika-aikar.

Kawo yanzu babu wata sanarwa da hedikwatar Hukumar Shige da Ficen ta fitar dangane da faruwar lamarin.

Sai dai wani jami’anta a hedikwatar da ke Abuja ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa a jira hukumar ta fitar da sanarwa a hukumance.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: David Shikfu Parradang garkuwa da mutane Hukumar Shige da Fice Hukumar Shige da

এছাড়াও পড়ুন:

Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF

Alƙaluman Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya ce Isra’ila ta kashe ƙananan yaran da yawansu ya kai 322 cikin kwanaki 10 da suka gabata a hare-haren da suke ci gaba da kai wa sassan Gaza.

Alƙaluman da UNICEF ta fitar ta ce a jimilla ƙananan yara fiye da dubu 15 ne Isra’ilan ta kashe cikin kusan watanni 18 da ta shafe tana yiwa yankin na Gaza luguden wuta, kuma daga lokacin da ƙasar ta katse yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakaninta da Hamas ta kashe ƙananan yaran da yawansu ya kai 322 tare da jikkata 609.

Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha Haaland zai yi jinyar mako bakwai — Guardiola

A cewar UNICEF galibin ƙananan yaran da Isra’ila ta kashe, na rayuwa ne a sansanonin wucin gadi bayan da hare-haren ƙasar ya rusa gidajensu tare da tilasta musu barin muhallansu.

Cikin adadin yaran har da tarin waɗanda Isra’ilan ta kashe suna tsaka da bukukuwan Sallah wato a ranar idi da washegari, galibinsu sanye da tufafi da kuma adon sallah kamar yadda hotuna suka nuna.

A cewar UNICEF yanzu haka akwai jumullar ƙananan yara fiye da dubu 34 da Isra’ilan ta jikkata, cikinsu har da waɗanda yanayi ke nuna yiwuwar sai an yanke musu wani sashe na jikinsu, a dai dai lokacin da ake fuskantar ƙarancin alluran kashe raɗaɗin ciwo a zirin na Gaza mai fuskantar ƙawanya.

Wannan alƙaluma na WHO na zuwa a daidai lokacin da Isra’ila ke amsa laifin cewa tabbas sojojinta ne suka buɗe wuta kan motar jami’an agaji kodayake Amurka ta ce laifin Hamas ne.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta miƙa Janar Tsiga da wasu ga NSA
  • Nasara A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda: Tattalin Arziƙin Jihar Zamfara Na Ƙara Haɓaka – Gwamna Lawal 
  • Sabbin Motocin Bas 100 Masu Aiki Da Lantarki Sun Fara Jigilar Fasinjoji A Birnin Addis Ababa
  • Janar Tsiga Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Bayan Shafe Kwanaki 56 A Hannun ‘Yan Bindiga 
  • Janar Tsiga ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga
  • Babban daraktan hukumar IAEA, Rafael Grossi, zai ziyarci Iran cikin makwanni masu zuwa
  • Iran Ta Bukaci Hukumar IAEA Ta Bayyana Matsayinta A Shirin Makamashin Nukliya Na Kasar
  • Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF
  • Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Bukaci A Ci Gaba Da Tallafawa Mabukata Bayan Ramadan.
  • Gwamna Abba Ya Nemi A Bayyana Fuskokin Waɗanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Edo