DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana
Published: 5th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta.
Sai dai wasu watan kan zo musu da ƙalubale – ba don sun shirya mishi ba kuma ba don sun gaza shiryawa ba.
Wani rukunin waɗannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan rayuwar mata zawarawa musamman a watan Ramadana.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: auren zawarawa Ramadan zawarawa
এছাড়াও পড়ুন:
Jirgin Farko Daga Minna Zuwa Abuja Ya Nuna Haɗin Gwiwar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi – Minista
Shi dai filin jirgin saman, wanda gwamnatin Umaru Bago ta gina a Jihar Neja, an raɗa masa sunan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Jirgin kasuwancin na farko mallakin kamfanin Overland Air mai lamba 5N-CCN ya sauka ne da misalin ƙarfe 1:32 na rana.
Cikin fasinjojin akwai Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, Minista Mohammed Idris, tsohon Gwamnan Neja Dakta Babangida Aliyu, Ƙaramin Ministan Harkokin Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, da wasu manyan jami’an gwamnati.
Ministan ya yaba wa Shugaba Tinubu saboda samar da yanayin da ya bai wa filin jirgin damar fara aiki, yana mai cewa hakan na nuna jajircewar Shugaban Ƙasa wajen inganta ababen more rayuwa a faɗin ƙasar.
Haka kuma, Ministan ya jinjina wa Gwamna Bago bisa hangen nesa da jajircewar sa na buɗe Jihar Neja ga cigaban noma da kasuwanci da masana’antu da kuma inganta tattalin arzikin jihar.
Ya ce: “Dole ne mu yaba wa shugaban ƙasar mu kamar yadda gwamnan mu ya faɗa. Wannan haƙiƙa mafarki ne da ya zama gaskiya. Gwamnan ne ya sa hakan ya tabbata. Yana da kwaɗayin ganin Jihar Neja ta buɗe ƙofar cigaba ta fannin noma, kasuwanci, masana’antu da kuma bunƙasar tattalin arziki.”
A nasa jawabin, Gwamna Bago ya ce wannan jirgi na farko wani ɓangare ne na buɗe jihar zuwa ga duniya baki ɗaya.
Ya ce: “Shugabannin kamfanin Overland sun nuna karamci matuƙa wajen ba mu wannan sabon jirgi daga Legas zuwa Minna, sannan yanzu daga Minna zuwa Abuja, kuma hakan zai riƙa faruwa sau uku a mako – a ranakun Litinin, Laraba da Juma’a. Wannan jirgi ne na buɗe hanya – buɗe Jihar Neja ga sararin samaniyar duniya.
“Muna son gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda filin jirgin ya samu suna daga gare shi, saboda ya ba mu dukkan goyon bayan da muke buƙata.”
Gwamna Bago ya ƙara da cewa jihar tana da niyyar amfani da filin jirgin wajen fitar da kayan amfanin gona zuwa ƙasashen waje don haɓaka tattalin arzikin jihar da zama ɗaya daga cikin manyan masu fitar da kayan noma daga Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp