Aƙalla fasinjoji 16 suka ƙone ƙurmus, yayin da wasu uku suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku ranar Talata a Jihar Ogun.
Aminiya ta ruwaito cewa hadarin wanda ya rutsa da mota ɗaya kacal ya afku ne a gidan Buhari da ke kan titin Abeokuta zuwa Shagamu.
DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana ‘A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice’An bayyana cewa, hatsarin dai ya rutsa da wata farar motar bas kirar Mazda mai lamba KJA 949 YJ, da misalin ƙarfe 1:00 na rana.
Kakakin Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar.
Ta ce ba za a iya tantance jinsin waɗanda abin ya shafa ba saboda “sun ƙone ƙurmus ta yadda ba a iya fahimtar halittar jikinsu ba.”
Okpe ta ɗora alhakin faruwar hatsarin a kan gobarar da ta tashi a cikin motar, tana mai cewa bas ɗin tana ɗauke da fasinjoji 21 da kuma wata tukunyar gas wadda ta yi bindiga a cikin motar.
“Hatsarin ya rutsa ne da mutane 21. Ba a iya tantance waɗanda abin ya shafa ba saboda sun ƙone ba a iya gane su ba.
“Mutane 16 ne suka mutu a hatsarin, yayin da uku suka samu raunuka daban-daban, sai kuma wasu biyu suka tsallake rijiya da baya.
“Abinda ake zargin ya haddasa hadarin shi ne gobarar da ta tashi a cikin motar, wadda kuma tana ɗauke da wata tukunyar gas, wanda ya kai ga fashewar,” in ji ta.
Okpe ta ce an kai waɗanda suka jikkata zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Idi Aba a birnin Abeokuta.
Kwamandan Hukumar FRSC na yankin, Akinwumi Fasakin, yayin da yake jajantawa iyalan mamatan, ya yi gargaɗin cewa, ya kamata a riƙa safarar kayan da ka iya jawo tashin wuta cikin kulawa da kuma motocin da aka keɓe waɗanda ƙwararru direbobi ke tuƙawa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hatsari Jihar Ogun
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa
Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 13 da suka ɓace yayin wani hatsarin jirgin ruwa a Jihar Bayelsa.
Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya yi karo da wani jirgin kamun kifi.
HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Muna samun galabar daƙile kwararowar baƙin haure — JamusMasu nutso a ruwa sun fara ƙoƙarin ceto waɗanda suka ɓace.
Bayanai sun nuna cewar wani jirgi mai suna ‘Meeting Marine’ wanda ya taso daga Anyama Ijaw zuwa Lubia da Foropa ya yi karo da jirgin kamun kifi.
Jirgin na da injin 115HP kuma wani mutum da ake kira Saturday ne yake tuƙa shi.
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ruwa a Bayelsa, Kwamared Ogoniba Ipigansi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa har yanzu ba a samo mutum 13 ba.
Ya ƙara da cewa matsalar rashin ingantaccen yanayin sadarwa a yankin na hana aikin ceto tafiya yadda ya kamata.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Bayelsa, DSP Musa Muhammad, ya ce ba a kai musu rahoton faruwar lamarin ba tukuna, amma sun fara bincike.