Mai barkwanci ya yi kuskuren liƙe bakinsa da sufa-gilu
Published: 5th, March 2025 GMT
Wasa ya koma kuka bayan da wani mai wasan barkwanci manne laɓɓansa ba sa buɗewa bayan da ya shafa musu gam din sufa-gilu a yayin da yake yin bidiyo kai-tsaye domin ƙayatar da masu bibiyarsa.
Mutumin ya shafa gilu ne, inda ya manne laɓɓansa, wanda cikin dakika kaɗan, mannewar ta kama fatar laɓɓan kamar yadda ya so, inda hakan ya sa yabar laɓɓansa a rufe sosai.
A zamanin da ake amfani da shafukan sada zumunta na zamani, mutane sukan yi iyakacin ƙoƙarinsu don samun mabiya da sakonsu zai kai gare su a intanet.
Raye-rayen zuwa abubuwan barkwanci, suna yin tasiri a shafukan sada zumunci na zamani.
Kwanan nan, wani bidiyo na wani mutum ɗan kasar Philippines ya ɗauki hankalin jama’a a intanet.
A cikin bidiyon, mutumin ya shafa sufa-gilu a laɓɓansa a matsayin wani ɓangaren na wasan barkwanci, amma lamarin ya sauya zuwa wani abun daban.
Bidiyon da tashar Talabijin ta Badis TV ta yada a shafin Insitagaram ya nuna wani mutumi zaune a cikin shago, rike da robar sufagilu kuma cikin wasa yana nuna kansa a kyamara.
Yana shafa shi, yana mannewa a lebbansa, amma cikin dakika kadan, mannewa ta kama fatun laɓɓansa yadda yake so, hakan dole ya sa ya bar laɓɓan a rufe sosai.
Da farko, mutumin ya bayyana yin hakan a matsayin nishadantarwa, yana dariya kamar ya yi nasara. Sai dai dariyarsa ta koma kuka, inda ya yi ta ƙoƙarin buɗe baki.
Nishadantarwarsa ta rikide zuwa firgici lokacin da ya gane laɓɓansa ba za su rabu ba, duk ya yi kokarin yin hakan.
Bayan wani lokaci sai hawaye hawaye suka fara gangarowa a fuskarsa yayin da yanayin ya yi tsanani, wanda hakan ya sa shi cikin damuwa.
Bidiyon ya sami ra’ayoyi sama da miliyan 6.7 na mabiya shafin kuma ya haifar da martani da yawa daga masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani.
Da yake mayar da martani ga bidiyon, wani mabiyin shafin ya yi dariya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Barkwanci
এছাড়াও পড়ুন:
Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba
Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba.
Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka yi ta taimakon kai don taimakawa matafiya a kan hanya.
Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya kama da wuta a Legas Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a FilatoGadar taimakon kai da aka gina a madadin babbar gadar da ta rufta watanni bakwai da suka gabata, ta kasance hanyar shiga ga masu ababen hawa da ke bin hanyar.
Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas ne ya bayar da kwangilar sake gina gadar a watan da ya gabata amma har yanzu ba a kai ga kwangilar zuwa wurin ba.
Masu ababen hawa da ke bin hanyar Jalingo da Wukari, an tilasta musu karkata zuwa hanyar garin Garba-Chede da ke ƙaramar hukumar Bali domin ci gaba da tafiya.
Masu ababen hawa da suka maƙale a ranar Laraba sun bayyana rashin jin daɗinsu kan gazawar gwamnatin tarayya na sake gina gadar kafin damina ta fara.
Wani direban babbar mota mai suna Bello Adamu ya ce direbobi da masu ababen hawa ba su ji daɗin yadda ba a sake gina gadar cikin lokaci mai kyau ba, kuma yanzu damina ta fara kawar da gadar wucin gadi a madadin babbar gadar.