Majalisar Zartarwa Ta Tarayyar Najeriya Ta Amince Da Kirkirar Sabbin Jami’oi 11
Published: 5th, March 2025 GMT
Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin bayar da lasisin kafa sabbin jami’o’i 11 a cikin kasar.
Ministan ilimi na kasar ta Nijeriya Tunji Alausa ya bayyana cewa; amincewa da kafa sabbin jami’oin da shugaban kasa ya yi, yana nuni ne da yadda ya mayar da hankali wajen ganin ilimi ya isa ga koma.
Wani abu da gwamnatin tarayyar ta amince da shi, shi ne ware kudade da su ka kai dala miliyan 1.67 domin harba tauraron dan’adam da zai rika kula da wuraren hako ma’adanai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati ta amince ta bai wa mahajjata kuɗin guzirinsu a hannu
Gwamnatin Najeriya ta amince kuma ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki.
Hakan ya biyo bayan tsoma bakin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi wanda ya roƙi shugaba Bola Tinubu a madadin maniyyatan ta hannun Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON.
Ficewar Kawu a jam’iyyarmu zai kawo zaman lafiya – Shugaban NNPP na Kano An kori lakcara kan neman lalata da ɗaliba matar aureHukumar NAHCON a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh, ta dage cewa ɓullo da hada-hadar kuɗi ta amfani da kati zai shafi shirin hukumar na gudanar da ayyukan hajjin 2025.
Shugaban ya damu matuƙa da cewa amfani da katin banki na dole da babban Bankin Najeriya CBN ya gabatar don gudanar da aikin hajji zai kawo tarnaƙi ga tsare-tsare da kuma gudanar da aikin Hajjin bana na 2025.
Bayan ganawar Hukumar NAHCON da Mataimakin shugaban ƙasa, Kwamishinan tsare-tsare da ayyukan kuɗi na NAHCON, Aliu Abdulrazaƙ, na cewa hakan zai bai wa mahajjan Najeriya damar kashe kuɗaɗensu da hannunsu yayin ibadar a Saudiyya.