Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza.

Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu a cikin kasarsu.

Sanarwar da aka wallafa a shafin ‘facebook’ ta kuma ce; Wancan labarun na karya ne babu kamshin gaskiya a cikinsu, tare da bayyana wadanda su ka watsa su da cewa, ba su yi aiki da mafi karancin ka’ida ta aikin watsa labaru ba, kuma manufar ita ce wasa da hankalin mutane.

Haka nan kuma ta ce wanda ya rubuta rahoton Jerome Kersey ba kwararren dan jarida ba ne, mutum ne wanda ya shahara da watsa labarun karya ba tare da dogaro da wata hujja ba.

Bugu da kari bayanin ya sake jaddada matsayar Libya akan batun Falasdinu da kare hakkokinsu na su yi rayuwa a cikin mutunci a cikin kasarsu.

Tun a ranar 25 ga watan Janairu ne dai shugaban kasar Amurka Donald Trump yake magana akan  fitar da Falasdinawa daga Gaza zuwa kasashen makwabta kamar Masar da Jordan,lamarin da kasashen biyu su ka yi watsi da shi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Manazarta A Iran Sun Gano Maganin Farfadiya Da Ciwon Rabin Kai

A karon farko manazarta a Iran sun yi nasarar samar da maganin farfadiya da kuma ciwon rabin kai

Gabanin wannan lokacin ana amfani da maganin “Topiramate” wanda ake shigo da sanadari mafi muhimmanci na hada shi daga waje, domin yinsa a matsayin kwayoyi da kuma kafso.

Wannan maganin ya sami karbuwa a matsayin na uku a bikin “Kharazmi” na shekara-shekara karo na 83.

Shugaban wannan shirin na samar da maganin Farajallah Mehna zadeh ya fada wa kamfanin dillancin labarun Fars cewa; Daya daga cikin magungunan shi ne “Topiramate”, sai dai an sami sabon salo na yin magani wanda zubin sanadarorin da ake hada shi ya banbanta da na baya.”

Farajallah Mehna Zadeh ya kuma ci gaba da cewa: Mun fara gudanar da bincike akan zubin sabbin  sanadarorin na magani a cikin dakunan bincike, kuma a karshe mu ka yi nasara.

Haka nan kuma ya ce; A karon farko a cikin Iran mun samar da sanadi mafi muhimmanci na hada wannan maganin a cikin gida wanda kuma ya kai ga yinsa cikin kwayoyi da kafso.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Karbi Lasisin Yin Kasuwanci Maras Shinge A Kan Iyakar Maigatari
  • Falasdinawa Kimani  80,000 Ne Suke Halattar Salla A Masallacin Al-Aksa A Cikin Watan Ramadan
  • Masar: An Kawo Karshen Taron Kasashen Larabawa Na Musamman Akan Gaza
  • Kremlin: Putin Ya Amince Da Shiga Tsakanin Iran Da Amurka
  • Nigeria: An Kafa Kwamitin Bincika Hanyoyin Kare Hatsurra Akan Doron Ruwa A Cikin Kasar
  • Syria: Sojojin HKI Sun Kai Wa Yankin Tartus Hari
  • Manazarta A Iran Sun Gano Maganin Farfadiya Da Ciwon Rabin Kai
  • Hasashe Kan Tarukan CPPCC Da NPC Na 2025
  • Gwamnatin Yamen Ta Gargadi HKI Da Amurka Kan Cewa Tana Sa Ido A Kan Abinda Ke Faruwa Da Tsagaita Wuta A Gaza