Babban magatakardar MDD Antonio Guterres  wanda ya halarci taron da kasashen larabawa suke yi a Masar, ya bayyana goyon bayansa ga tsarin da su ka bijiro da shi na sake gina yankin Gaza, ba tare da an fitar da Falasdinawa daga cikinsa ba.

Gutress ya ce; Ina maraba da kuma nuna cikakken goyon bayana ga shirin da taron kungiyar kasashen larabawa ta bijiro da shi na sake gina Gaza.

Gutrress ya kuma ce: MDD a shirye take ta shiga da karfi a yi wannan aikin da ita.

Haka nan kuma babban magatakardar MDD ya yi kira da a dauki duk matakin da ya kamata domin ganin ba a sake komawa yaki a Gaza ba.

Gutteres ya kuma ce, Gaza ba ta da makoma wacce ta wuce ta kasance a karkashin daular Falasdinawa.

Babban magatakardar MDD ya bayyana taron na kasashen larabawa da cewa yana da matukar muhimmanci domin daukar nauyi a jumlace da zai kai ga kawo karshen yakin Gaza.

A jiya Talata ne dai kasashen larabawa su ka hadu a Alkahira ta kasar Masar domin halartar taron tattauna hanyoyin sake gina Gaza da kuma kalubalantar manufar Amurka da HKI na korar Falasdinawa daga Gaza.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasashen larabawa

এছাড়াও পড়ুন:

Trump Ya Yi Barazanar Korar Daliban Da Ke Goyon Bayan Falasdinawa

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rage kudaden da gwamnatin tarayya ke ba wa kwalejoji da jami’o’in da ke ba da izinin ” zanga-zangar goyan bayan Falasdinawa tare da hukunta daliban da suka shiga irin wannan zanga zanga.

Trump ya yi wannan gargadin ne a wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta bayan da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa suka taru a harabar jami’ar Columbia da ke New York.

Shugaban na Amurka ya kara da cewa “za a daure masu tayar da hankali” ko dai a daure su ko kuma a tura su dindindin zuwa kasashensu na asali.”

Ko da yake bai ambaci musamman zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a cikin sakon nasa ba, amma a baya Trump ya yi barazanar korar duk daliban da suka shiga zanga-zangar adawa da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a zirin Gaza.

A karshen watan Janairu, Trump ya rattaba hannu kan wata doka da ta bukaci gwamnati ta kori daliban kasashen waje da suka shiga zanga-zangar goyon bayan Falasdinu.

Ya yi zargin cewa zanga-zangar da aka yi a harabar jami’ar ta haifar da “kyama, barna da kuma cin zarafi a kan ‘yan kasarmu, musamman a makarantunmu da harabar jami’armu.”

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da masana shari’a sun dage cewa wannan umarni ya saba wa ‘yancin fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Trump Ya Yi Barazanar Korar Daliban Da Ke Goyon Bayan Falasdinawa
  • Hamas Ta Yi Maraba Da Shirin Sake Gina Gaza Da Taron Kasashen Larabawa Ya Gabatar
  • Taron Kasashen Turai Don Goyon Baya Ga Kasar Ukraine, Ya Watse Ba Tare Da Tsaida Irin Taimakon Da Zasu Yi Mata Ba
  • Masar: An Kawo Karshen Taron Kasashen Larabawa Na Musamman Akan Gaza
  • Kasashen Larabawa Sun Yi Tir Da Matakin Isra’ila Na Hana Shigar Da Kayan Agaji A Gaza
  • Masar : Za’a Gabatar Da Shirin Baiwa Falasdinawa Yancin Zama A Kasarsu
  • Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Shirin Ciyarwar Na Watan Ramadan
  • Gwamnatin Yamen Ta Gargadi HKI Da Amurka Kan Cewa Tana Sa Ido A Kan Abinda Ke Faruwa Da Tsagaita Wuta A Gaza
  • Masar Za Ta Bayyana Shirin Sake Gina Gaza A Yayin Taron Larabawa