Masar: An Kawo Karshen Taron Kasashen Larabawa Na Musamman Akan Gaza
Published: 5th, March 2025 GMT
Kungiyar kasashen larabawa ta kawo karshen taron musamman da ta yi a birninn alkahira akan Gaza, tana mai amincewa da shawarar kasar Masar akan yadda za a sake gina yankin na Gaza.
Bayanin bayan taron kungiyar ya kunshi cewa, shirin sake gina Gaza, yana nufin sake hade yankin da yammacin kogin Jordan a karkashin iko daya.
Mahalarta taron na Masar sun kuma nuna kin amincewarsu da duk wani shiri na dauke mutane Gaza zuwa wani wuri na daban.
Shi kuwa Fira ministan Falasdinu Muhammad Mustafa ba bayyana fatansa na ganin ai an aiwatar da shirin na sake gina Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Bude Taron Dandalin Tattaunawar Afirka Ta Yamma Karo Na Farko A Senegal
A nasa bangare kuma, firaministan kasar Senegal Ousmane Souko ya bayyana cewa, kasar Senegal tana son hadin gwiwa da cibiyar nazarin ilmin kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin don kara cudanyar juna da gudanar da ayyukan nazarin ilmi tare, baya ga samar wa kasashen dake yammacin nahiyar Afirka dabarun neman samun ci gaba.
Bugu da kari, shugaban kwalejin nazarin hukumomin kasar Senegal ya ce, aikin kulla yarjejeniyar kafa cibiyar nazarin Sin da Afirka cikin hadin gwiwa, ya shaida yadda hadin gwiwar kwararru a tsakanin Sin da Afirka ya kai wani sabon matsayi. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp