Aminiya:
2025-03-06@03:39:24 GMT

Mijina bai hana ni waƙa ba sai dai… – Fa’iza Badawa

Published: 5th, March 2025 GMT

Fa’iza Muhammad wacce aka fi sani da Fa’iza Badawa, daya ce daga cikin mawakan Kannwood.

Ita ta yi wakar fim din Oga Abuja, daya daga cikin finafinan suka yi tashe, ya kuma fito da basirar mawakiyar.

Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Mai barkwanci ya yi kuskuren liƙe bakinsa da sufa-gilu

Kasancewar ta yi aure, mutane sun ɗauka ta daina harkar waƙa baki ɗaya.

Sai a hirarta da wakilinmu Ibrahim Musa Giginyu, Fa’iza ta ce ba haka ba ne.

Yaushe kika yi aure?

Na yi aure ne a ranar 8 watan Afrilun shekar 2017, kuma ina zaune lafiya da mijina da kuma haihuwa daay da Allah Ya bamu, kuma aure ne na so ada kauna da kuma kyakkyawar kulawa. Kuma yana taimaka min tare da goya min baya a abubuwan ada na ke yi.

Shin gaskiya ne cewa auren ne ya hana ki ci gaba da waka?

Ba gaskiya ba ne. Har yanzu ina yin waka, kuma duk wasu manya-manya da ke wannan sana’a sun san har yanzu ina yin waka saboda muna aiki tare.

Duk lokacin da suke bukatar aiki da ni, su kan kira ni ko kuma su kira mijina tare neman izininsa na mu yi aiki ko aika masa sako zuwa gare ni.

Mu mawaka a bayan fage muke, ba ganinmu ake yi ba, sai dai a ji muryoyinmu wanda da shi a ke gane mu, da kuma cewa, yawancinmu mawaka mata da zarar mun yi aure sai mu daina aiki, shi ya sa da yawa suka dauka nima na daina waka.

A lokuta na kan yi wa abokan aikina bayani cewa, ina nan, na kuma ci gaba da sana’ata ta waka a wannnan masana’antar tamu.

Shin ko yaya ki ke tafiyar da wannan sana’a a yanzu da kina matar aure?

Wani tsari na fito da shi la’akari da tsarin addinina da kuma kula da matsayina a inda na kan bukaci duk mai son in yi mi shi waka da ya je ya gama rubuta wakarsa, ya kuma gama shiririnsa da wurin daukar murya.

Idan ya yi hakan, sai in nemi a sa min ranata ni kadai da zan je in yi nawa baitukan ko kuma dora murya. Inda na gama sai su ci gaba da sauran wadanda za su yi da su.

Kuma ya kamata ka sani cewa, ba ni kadai ce na ke da aure ba, na kuma ke waka, domin muna da yawa a yanzu fiye da yadda ka ke tunani.

Ka ga da akwai Zuwairiya Isma’ila, da Murja Baba, da Naja’atu Ta’Annabi, da Maryam A Baba, da Jamila Sadi, da Zainab Diamond, da Sa’a Bocal, da kuma Sa’a Nazifi Asnanic. Da sauransu.

Wane kalubale ne kike fuskanta a matsayinki na mawakiya kuma matar aure?

Ni babu wata matsala da na ke fuskanta a matsayina na matar aure kuma mai sana’ar waƙa musamman ma a gidan mijina.

Domin akwai kyakkyawar fahimta tsakanina da shi, bayan so da kauna, ya na bani sharwari tare da tallafa min a duk al’amurana ciki har da wannan sana’a ta waka.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Fa iza Badawa kannywood Waƙa

এছাড়াও পড়ুন:

Yemen Ta Gargadi HKI Kan Ci Gaba Da Hana Shigar Kayakin Agaji Zuwa Yankin Gaza

Ana cikin zullumi kan sake barkewan yaki a Gaza, bayan da HKI ta ci gaba da hana shigowar kayakin zuwa cikin Gaza. Sannan kungiyar Ansarull ta kasar Yemen ta yi barazanar daukar mataki a kan HKI idan ta ci gaba da hana shigar kayakin Agaji zuwa cikin gaza.

Abdullatif Al-washali wani dan siyasa a kasar ta Yemen ya bayyana cewa rufe mashigar Rafah ta inda kayakin agaji suke wucewa su shiga Gaza, wata hanya ce ta wahalarta mutanen yankin, kuma yana dai dai da cilla yaki a kan mutanen Gaza. Ya ce kasar Yemen tana iya daukar matakin soje kan HKI matukar wannan tocewar ta ci gaba.

Har’ila yau sojojiun kasar ta Yemen sun bayyana cewa inda HKI ta ci gaba da sabawa yarjeniyar da suka cimma da Falasdinawa a Gaza, sojojin suna iya daukar matakai wadanda zasu shafi cibiyoyin tsaro na HKI a cikin kasar Falasdinu da ta mamaye ko na wajen kasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Kano ta yi wa dokar hukumar tace fina-finai gyaran fuska
  • Yemen Ta Gargadi HKI Kan Ci Gaba Da Hana Shigar Kayakin Agaji Zuwa Yankin Gaza
  • Matar Aure Ta Shiga Hannu Kan Zargin Kashe Kishiyarta A Bauchi
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Rage Lokutan Aiki Ga Ma’aikatan Jihar
  • Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata
  • Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki
  • RAMADAN: Gwamnatin Jigawa Ta Rage Lokutan Aiki Ga Ma’aikatan Jihar 
  • Syria: Sojojin HKI Sun Kai Wa Yankin Tartus Hari
  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Gargadi Malaman Da Ba Sa Zuwa Aiki