Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Rage Lokutan Aiki Ga Ma’aikatan Jihar
Published: 5th, March 2025 GMT
Gwamna Umar Namadi ya rage lokutan aiki ga ma’aikatan jihar Jigawa a wannan lokaci na azumin watan Ramadan na shekarar 2025.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri ya sanyawa hannu, aka kuma bai wa gidan rediyon Najeriya a Dutse.
“Ma’aikatan jihar za su je aiki karfe 9 na safe sannan su tashi da karfe 3 na rana daga ranar Litinin zuwa Alhamis maimakon zuwa karfe 5 da ake kai wa a baya, sai ranar Juma’a ma’aikatan za su je aiki da karfe 9 na safe su tashi da karfe 1 na rana kamar yadda aka saba”.
Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa, an yi wannan karimci ne da nufin samarwa ma’aikatan gwamnati damammaki masu yawa na shirye-shiryen hutun watan Ramadan da kuma kara himma wajen gudanar da ayyukan ibada da ke da alaka da wannan wata mai alfarma.
“Ana fatan ma’aikatan gwamnati a jihar za su yi amfani da lokacin watan Ramadan wajen yi wa jiharmu addu’a da neman albarkar Ubangiji,” in ji shugaban ma’aikatan.
Alhaji Muhammad Dagaceri ya kara jaddada bukatar ma’aikatan gwamnati su yi amfani da lokacin azumi wajen yin addu’ar zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin jihar da ma Najeriya baki daya.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Karbi Lasisin Yin Kasuwanci Maras Shinge A Kan Iyakar Maigatari
Gwamna Mallam Umar Namadi na jihar Jigawa ya karbi lasisin yin hada hadar kasuwanci na kasa da kasa, wato kasuwanci maras shinge a kan iyakar Maigatari a hukumance, wanda hukumar kula da sarrafa kayayyaki ta Najeriya NEPZA ta bayar kwanan nan.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa manema labarai a Dutse.
Ya bayyana cewa, kwamishinan kasuwanci, da masana’antu, Alhaji Aminu Kanta ne ya mika wa Gwamna Umar Namadi lasisin a ofishinsa.
Hamisu Mohammed Gumel ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kafa wannan gwamnati mai ci ta dukufa wajen gudanar da aikin karbar lasisin aikin daga NEPZA
A cewarsa, wannan ya nuna karara da kudurin gwamnati na bunkasa tattalin arziki, da inganta harkokin kasuwanci, da kuma sanya jihar Jigawa a matsayin babbar cibiyar zuba jari da bunkasa masana’antu.
Sakataren yada labaran ya yi nuni da cewa, kafa harkar cinikayya a kan iyakar Maigatari na da nufin jawo hankalin masu zuba jari na gida da waje, da inganta samar da ayyukan yi, da bunkasa harkokin kasuwanci, musamman a yankin arewacin Najeriya.
Ya ce, Gwamna Namadi ya nuna jin dadinsa ga kokarin hadin gwiwa da ya kai ga samun lasisin tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da yanayi mai kyau don gudanar da kasuwanci yadda ya kamata.
Hamisu ya yi nuni da cewa, a karkashin gwamnatin Gwamna Umar Namadi, wannan yunkuri ya samu gagarumin ci gaba da nufin bunkasa tattalin arziki da habaka masana’antu a jihar.
Kwamishinan ya samu rakiyar Kodineta na shiyyar kasuwanci maras shinge ta Maigatari, Abdulaziz Usman Abubakar da mai kula da shiyyar Bello Abdullahi Nura.
Usman Muhammad Zaria