’Yan sanda sun ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a Gombe
Published: 5th, March 2025 GMT
’Yan sanda sun ceto wani mutum mai shekaru 48, Alhaji Samaila Muhammed, da aka yi garkuwa da shi a ƙauyen Lano da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba ta Jihar Gombe.
An gudanar da aikin ceton bisa tsari tare da haɗin gwiwar ‘yan banga na yankin, lamarin da ya tabbatar da cewa mutumin ya shaƙi iskar ’yanci salin-alin.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahukunta sun tabbatar da ƙoshin lafiyarsa sannan daga bisani aka sada shi da ’yan uwansa.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
DSP Buhari ya tabbatar wa jama’a cewa za a ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ayyukan laifi a jihar.
Sanarwar ta kuma gode wa jama’a bisa haɗin kansu tare da yin kira da su kasance masu sa ido, su kuma riƙa sanar da hukuma game da duk wani abu da suka ga ya dace ko ya saɓa da al’ada a cikin al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda garkuwa da mutane jihar Gombe
এছাড়াও পড়ুন:
An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu a Kudu
An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP).
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito ne daga ƙauyen Minda da ke Ƙaramar hukumar Lau a Jihar Taraba.
Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52 Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a BornoA yayin da take zantawa da manema labarai a Jalingo, ranar Juma’a ta ce an yaudari yaran daga unguwar su aka yi safarar su zuwa jihohin Kudu maso Gabas.
Ta ce, sun gano su kuma sun ceto su a garin Aba, a Onitsha da kuma wani ɓangare na Jihar Imo tare da iƙirarin waɗanda suka yi safarar su da cewa su marayu ne.
Ta bayyana cewa, an damƙe masu aikata safarar ne a garin Gembu da ke ƙaramar hukumar Sardauna, a lokacin da suke gudanar da haramtattun aikinsu, wanda ya kai ga ceto yaran takwas, yayin da wasu da dama da aka yi safarar su ba a kai ga ceto su ba.
Waɗanda aka yi safarar ta su a ƙarshe sun sake haɗuwa da iyayensu a watan Maris 2025, sun tabbatar da cewa an sayar da su ba tare da sanin iyayen su ba.
“Bayan ɗaukar matakin gaggawa da ma’aikatar ta yi da kuma Hukumar NAPTIP, an dawo da takwas daga cikin yaran Jihar Taraba cikin lafiya.