EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700
Published: 5th, March 2025 GMT
Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel kan zargin almundanar naira biliyan 700.
EFCC ta tsare tsohon gwamnan ne bayan ya amsa gayyatar ta a ranar Talata domin amsa wasu tambayoyi kan zargin karkatar da kuɗi da wata ƙungiya mai rajin yaƙi da masu zamba ta yi masa.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa tsohon gwamnan ya karɓi naira tiriliyan uku daga asusun Gwamnatin Tarayya a tsawon shekara takwas da ya yi yana mulki, amma ya bar wa jihar bashin naira biliyan 500 da rashin biyan kuɗin wasu ayyuka na naira biliyan 300 bayan ya sauka.
Haka kuma, ƙungiyar ta zargi Mista Emmanuel da kasa yin bayani kan yadda aka kashe wasu maƙudan kuɗi har naira biliyan 700 kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.
Emmanuel ya kasance Gwamnan Akwa Ibom daga 2015 zuwa 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
A ranar Juma’ar da ta gabata ma EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan Abia, Theodore Orji da wasu mutum huɗu a gaban kotu, bisa zargin ɓarnatar da kusan naira biliyan 47.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Akwa Ibom tsohon Gwamnan naira biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Fashi Da Makami Sun Kashe Tsohon Babban Kwanturolan Hukumar NIS A Abuja
Parradang ya yi aiki a hukumar NIS fiye da shekaru 30, inda ya yi aiki a fadin jihohin kasar nan da suka hada da Kano, Legas, Kwara, Enugu, da Abuja. Ya halarci kwasa-kwasan ƙwararru da yawa a cikin gida da waje.
Domin karrama shi da hidimar da ya yi, an karrama shi da lambar yabo ta kasa ta jami’in tsaro na Tarayya (OFR) kuma ya yi fice a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru (NIPSS).
Hukumomin tsaro tuni suka fara gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi masa, inda ake kokarin zakulo wadanda suka aikata laifin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp