Yemen Ta Gargadi HKI Kan Ci Gaba Da Hana Shigar Kayakin Agaji Zuwa Yankin Gaza
Published: 5th, March 2025 GMT
Ana cikin zullumi kan sake barkewan yaki a Gaza, bayan da HKI ta ci gaba da hana shigowar kayakin zuwa cikin Gaza. Sannan kungiyar Ansarull ta kasar Yemen ta yi barazanar daukar mataki a kan HKI idan ta ci gaba da hana shigar kayakin Agaji zuwa cikin gaza.
Abdullatif Al-washali wani dan siyasa a kasar ta Yemen ya bayyana cewa rufe mashigar Rafah ta inda kayakin agaji suke wucewa su shiga Gaza, wata hanya ce ta wahalarta mutanen yankin, kuma yana dai dai da cilla yaki a kan mutanen Gaza.
Ya ce kasar Yemen tana iya daukar matakin soje kan HKI matukar wannan tocewar ta ci gaba.
Har’ila yau sojojiun kasar ta Yemen sun bayyana cewa inda HKI ta ci gaba da sabawa yarjeniyar da suka cimma da Falasdinawa a Gaza, sojojin suna iya daukar matakai wadanda zasu shafi cibiyoyin tsaro na HKI a cikin kasar Falasdinu da ta mamaye ko na wajen kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Bayan Cece-ku-ce Da Zelenskyy, Trump Ya Dakatar Da Tallafin Soji Ga Ukraine
Sai dai, Firaministan Ukraine Denys Shmyhal ya ce, har yanzu Kyiv na da isassun makamai da za ta kai wa dakarunta dake yaki a gaba-gaba.
“Taimakon kayayyakin Soji na Amurka yana da mahimmanci kuma yana ceton dubban rayuka, don haka, Kyiv za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta ci gaba da alaka da Washington”. In ji Shmyhal
Shmyhal ya kara shaida cewa, “Muna da mafita ɗaya kawai – nasara don tsira. Ko dai mu ci nasara, ko kuma wani ya rubuta mana shiri na biyu.”
A nata bangaren, fadar Kremlin ta Rasha ta ce, katse tallafin soji ga Ukraine shi ne matakin da ya fi dacewa don samar da zaman lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp