Taron Kasashen Turai Don Goyon Baya Ga Kasar Ukraine, Ya Watse Ba Tare Da Tsaida Irin Taimakon Da Zasu Yi Mata Ba
Published: 5th, March 2025 GMT
Shuwagabannin kasashen Turai da wakilai daga kasashe 19 na Kungiyar, sun kammala taro a birnin Lodon, inda suka nuna goyon bayansu ga kasar Ukraine, musamman kan yadda ya dage wajen kare kasarsa da kasashen Turai a gaban Donal Trum a ranar Jumma’an da ta gabata, ya waste ba tare da kasashen sun bayyana abinda zasu iya yiwa Ita Ukraine a yakin da take ci gaba da fafatawa da Rasha ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa matsalolin da suka taso dangane da dogaron da kasashen turai suke yi kan kungiyar Tsaro ta NATO yana daga cikin manya-manyan al-amura da suka tattauna.
Yakin cacarbakin da shugaba Trump na Amurka yayi da shugaban kasar Ukraine ya zama masomin kawo sauye-sauye masu yawa a dangantakar kasashen da Amurka.
Firai ministan kasar Ukraine Keir Starmer ya gabatar da shawara mai matakai 4 ta taimakawa kasar ta Ukraine a yakin da taek fafatawa da kasar Rasha. Sannan shuwagabannin kasashen turai sun bukaci a samar da wata cibiyar tsaron kasashensu ba tare da dogaro da kasar Amurka ba.
Har’ila yau shugaban kungiyar tarayyar ta Turai Ursula Von der Leyen ya bukaci a gaggauta samar da hanyar tsaron kasashen na turai da gaggawa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasashen Turai kasar Ukraine
এছাড়াও পড়ুন:
Arsenal Ta Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya bayyana farin cikinsa akan wannan tarihi, inda yace abu mafi muhimmanci shi ne ganin cewar Arsenal na da babbar damar tsallakawa zuwa matakin na kusa da na kusa da na karshe duk da cewar akwai jan aiki idan PSV ta ziyarci Arsenal a gidanta inji Arteta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp