Aminiya:
2025-03-06@03:33:17 GMT

Wata mata ta kashe kishiyarta a Bauchi

Published: 5th, March 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure.

Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025.

Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700

Sai dai ya ce ’yan uwan mamaciyar suna zargi kishiyarta da hannu a mutuwarta.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Binciken farko ya kai ga kama kishiyar mamamciyar, mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28.

Da aka tambaye ta, ta amsa cewar ta shaƙe Hajara har lahira, sannan ta zuba mata ruwan zafi da ƙone gawarta don ɓoye laifinta.

Rundunar ta bayyana cewa za a ci gaba da bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID).

Hakazalika, rundunar ta ce idan buƙatar tono gawar ta taso domin yin ƙarin bincike, za ta yi hakan don tabbatar da gaskiya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Kishiya

এছাড়াও পড়ুন:

NOA Ta Kara Daura Damarar Inganta Ayyukanta A Jihar Jigawa

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul  tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa.

Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan gwamnati na Dutse.

Ya jaddada cewa, hukumar za ta iya yin nasara ne kawai a jihar idan masu ruwa da tsaki kamar ofishin babban sakataren yada labaran suka hada hannu da ita.

Malam Tijjani Ibrahim ya ci gaba da bayanin cewa, makasudin ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa  tsakanin NOA da ofishin sakataren, a fannin wayar da kan jama’a game da manufofi da tsare-tsare daban-daban na gwamnatin Jihar Jigawa a dukkan matakai.

A cewarsa, a shekarar 2024, NOA ta yi kokari sosai wajen wayar da kan jama’a kan katin shaidar dan kasa da kuma tsohon taken kasa da aka sake dawo da shi.

Don haka Tijjani ya jaddada cewa akwai bukatar a kara kaimi domin ganin Najeriya ta kara samun hadin kai da wadata kasa.

Da yake mayar da martani, babban sakataren yada labarai, Hamisu Mohammed Gumel ya yabawa NOA bisa wannan ziyarar.

Ya kuma yi alkawarin ci gaba da ba da goyon baya da hadin kai don cigaban bangarorin 2.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a Bauchi
  • Ana zargin wata mata da kashe kishiyarta a Bauchi
  • NOA Ta Kara Daura Damarar Inganta Ayyukanta A Jihar Jigawa
  • Matar Aure Ta Shiga Hannu Kan Zargin Kashe Kishiyarta A Bauchi
  • Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa Da Taɓarya A Bauchi
  • Miji ya yi yunƙurin kashe matarsa kan zargin maita
  • Faransa Da Burtaniya Sun Ba Da Shawarar Tsagaita Wuta Na Wata Guda A Ukraine
  • Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda
  • Junbilat: ‘Yan Sahyoniya Suna Son Tarwatsa Kasar Syria