Ana zargin wata mata da kashe kishiyarta a Bauchi
Published: 5th, March 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure.
Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025.
Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700Sai dai ya ce ’yan uwan mamaciyar suna zargi kishiyarta da hannu a mutuwarta.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.
Binciken farko ya kai ga kama kishiyar mamamciyar, mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28.
Da aka tambaye ta, ta amsa cewar ta shaƙe Hajara har lahira, sannan ta zuba mata ruwan zafi da ƙone gawarta don ɓoye laifinta.
Rundunar ta bayyana cewa za a ci gaba da bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID).
Hakazalika, rundunar ta ce idan buƙatar tono gawar ta taso domin yin ƙarin bincike, za ta yi hakan don tabbatar da gaskiya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu
Fitaccen malamin addinin Islama da ke Jihar Bauchi, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya riga mu gidan gaskiya.
Almajiransa sun tabbatar wa Aminiya cewa ya rasu ne a gidansa da ke Bauchi inda za a yi jana’izarsa a safiyar wannan Juma’ar.
Malamin ya yi fama da rashin lafiya inda gabanin watan Ramadana ya fita neman magani a ƙasashen Masar da Saudiyya.
Fitowarsa ta ƙarshe ita ce ranar Idin ƙaramar Sallah da ta gabata, inda ya yi huɗuba kan muhimmanci haɗin kai a tsakanin musulmi.