Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a Bauchi
Published: 5th, March 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta cafke wani matashi Safiyanu Dalhatu, mai shekara 20, kan zargin kashe mahaifiyarsa har lahira a unguwar Abujan Kwata.
Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ’yan Kwamitin Tsaro na Unguwar ne suka kai rahoton lamarin ofishin rundunar na ‘A’ Division da ke Bauchi.
Bincike ya nuna cewar mahaifiyar matashin, Salama Abdullahi, mai shekara 40, ta samu karaya a hannayenta biyu sakamakon dukan da ya mata bayan sun samu saɓani.
Bayan samun rahoto, jami’an rundunar ƙarƙashin jagorancin CSP Abdullahi Muazu, sun garzaya wajen da lamarin ya faru.
Sun kai Salama Asibitin ATBUTH da ke Bauchi, amma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarta.
Bincike ya nuna cewa matashin ya yi amfani da wani abu wajen dukan mahaifiyar tasa.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin.
Kuma ya ce da zarar bincike ya kammala, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi
Dubban mutane ne suka halarci jana’izar shahararren malamin addinin Musuluncin nan kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, Sheikh Dokta Idris Abdulaziz.
Malamin ya rasu ne a ranar Alhamis a gidansa da ke Bauchi bayan fama da doguwar rashin lafiya.
Kotun ƙoli ta sauke Julius Abure daga shugabancin jam’iyyar LP Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce — WikeYa je ƙasashen Masar da Saudiyya domin neman magani kafin watan Ramadan.
Tun da safiyar ranar Juma’a, ɗaruruwan ɗalibansa da mabiyansa daga Bauchi, maƙwabtan garuruwa da kuma wasu jihohi sun taru a gidansa domin halartar jana’izarsa.
An gudanar da sallar jana’izar a ranar Juma’a a filin Idi na Games Village.
Manyan malamai, ’yan siyasa, ’yan uwa da abokan arziƙi da kuma mazauna birnin Bauchi sun halarci jana’izar.
Aminiya ta ruwaito cewar lokaci na ƙarshe da aka gan shi a bainar jama’a shi ne a ranar Sallah, inda ya yi wa al’ummar Musulmi jawabi bayan sallar Idi, inda ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da juna.
Ga hotunan yadda jana’izar ta gudana: