Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Dahiru Liman, ya raba kayayyakin agaji na watan Ramadan na sama da Naira miliyan 200 ga al’ummar mazabarsa.

Ya yi hakan ne da nufin tallafa wa al’umma domin samun damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki, duba da halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki.

A wajen bikin kaddamar da rabon, Yusuf Dahiru Liman, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan ofishinsa, Bashir Adamu Nababa, ya jaddada aniyarsa ta rage wahalhalun da al’ummar mazabarsa ke fuskanta.

Ya bayyana rabon kayayyakin a matsayin wani bangare na alkawarin da ya dauka na inganta walwalar jama’a a yayin  yakin neman zabe.

Shugaban kwamitin masu ruwa da tsaki, Isiyaku Adamu Nababa, ya jaddada cewa shirin ya nuna irin sadaukarwar da shugaban majalisar yake yi na yi wa al’ummarsa hidima baya ga  ayyukan majalisa.

Ya bayyana sauran ayyukan jin kai da Yusuf Liman ya jagoranta, da suka hada da ayyuka a fannin ilimi, da  kiwon lafiya, da kuma sanin makamar aiki.

Da yake jawabi a wajen taron, Hakimin Barnawa, Alhaji Kabiru Zubairu, ya bayyana jin dadinsa bisa jajircewar da kakakin majalisar ya yi wajen kyautata rayuwar al’ummar mazabarsa.

Ya yaba da yadda shugaban majalisar ke gudanar da jagoranci, wanda ke tafiya da kowa ba tare da  bambancin addini ko kabila ba.

Shi ma mataimakin shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Nehemiah Baba Karik, ya yaba da yadda Shugaban Majalisar yake aiki ba tare da nuna son kai ba, inda ya ce yana yi wa dukkan mazauna yankin hidima bisa adalci.

A nasa jawabin,  Shugaban Majalisar Limamai da Malamai na mazabar Makera Malam Ibrahim Mahe, ya yaba da wannan karamci, inda ya ce ya zo a daidai lokacin da dace.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya sakawa shugaban majalisar bisa kokarinsa na tallafawa al’ummar jihar Kaduna.

Wadanda suka ci gajiyar wannan karimcin sun hada da malamai maza da mata na makarantun islamiyya, da manyan limamai, da  kungiyoyin Nisa’us Sunnah na Barnawa, da Makera, da Kakuri, da masu rike da  sarautun gargajiya, da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, da sauransu.

Sauran sun hada da hukumomin tsaro da suka hada da rundunar sa kai ta  Civilian JTF, da kuma kungiyoyin agaji na  JIBWIS, da  Fityanul Islam, da Jama’atu Nasril Islam da dai sauransu.

Da dama daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin sun nuna matukar godiya ga wannan karamcin, inda suka yi addu’o’in Allah ya ci gaba da yi ma shugaban majalisar jagoranci da samun nasara a ayyukansa.

 

Shamsuddeen Mannir Atiku

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Tallafin Ramadan Shugaban Majalisar shugaban majalisar

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Jigawa Ta Yi Garambawul Ga Dokar Bada Tallafi Ga Masu Bukata Ta Musamman

Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta yi garambawul ga dokar bada kudaden tallafi ga masu bukata ta musamman domin kara yawan kudaden tallafin  daga naira dubu bakwai zuwa naira dubu goma.

Daukar wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamatin kula da al’amuran mata da cigaban al’umma na majalisar.

Da yake gabatar da rahotonsa, shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Birnin Kudu, Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim, yace kwamatin ya tattauna da masu ruwa da tsaki domin duba bukatar kara yawan kudaden da ake tallafawa masu bukata ta musamman daidai da halin da rayuwa ta ke ciki a yau.

Ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar ya hada da kara yawan makafi da kurame da kutare da sauran  masu bukata ta musamman da ke amfana da wannan tallafi daga mutane 150 zuwa 200 a dukkan kananan hukumomin jihar 27.

Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim ya yi nuni da cewar, karin yawan tallafin da kuma wadanda su ke amfana na daga cikin kudurin gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta rayuwar masu rauni a cikin al’umma.

Ya bukaci dukkan masu bukata ta musamman a fadin jihar, su ci gaba da gudanar da addu’oi ga gwamnatin jihar da sauran shugabanni domin samun sukunin sauke nauyin da ke kan su tare da wanzuwar zaman lafiya da cigaban tattalin arziki da zamantakewa a Jigawa da Najeriya ba ki daya.

Bayan Akawun majalisar, Barrister Musa Aliyu Abubakar ya gudanar da karatu na 3 akan kudurin, sai shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya sanar da amincewa da kudurin ya zamo doka.

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jihar Jigawa Ta Yi Garambawul Ga Dokar Bada Tallafi Ga Masu Bukata Ta Musamman
  • Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio
  • Zargin Cin Zarafi: Natasha ta gabatar wa majalisa ƙorafinta game da Akpabio
  • An Bude Taron Shekara-shekara Na Majalisar Dokokin Kasar Sin
  • Ɗan majalisa ya biya wa ɗaliban mazaɓarsa N45m na jarabawar WAEC
  • Meranda Ta Yi Murabus, Obasa Ya Sake Zama Kakakin Majalisar Dokokin Legas
  • Tawagar ECOWAS Ta Fice Daga Guinea-Bissau Bayan Barazana Daga Shugaban Kasar
  • HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja
  • Ramadan: Coci ya ciyar da Musulmi 1,000 a Kaduna