Aminiya:
2025-03-06@03:38:29 GMT

Zargin Cin Zarafi: Natasha ta gabatar wa majalisa ƙorafinta game da Akpabio

Published: 5th, March 2025 GMT

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta gabatar da ƙorafinta a gaban Majalisar Dattawa kan Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, bisa zargin cin zarafi da kuma tauye mata haƙƙi a majalisa.

A ranar 20 ga watan Fabrairu ne rikici ya ɓarke a zauren majalisar, lokacin da Shugaban Majalisar, Akpabio, ya umarci wani ma’aikacin majalisa da ya fitar da Sanata Natasha daga zauren, bayan da aka ce ta ƙi komawa sabuwar kujerar da aka ware mata.

Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a Bauchi Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe

Wannan lamarin ya jawo suka daga ƙungiyoyi da mutane da dama, inda suka nemi a yi bincike kan abin da ya faru.

Abin da Sanata Natasha Ta Gabatar Wa Majalisa

Sanata Natasha ta gabatar da ƙorafinta ga Majalisar Dattawa, inda ta ce: ’Ina gabatar da ƙorafi kan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, bisa cin zarafi na lalata da kuma amfani da muƙaminsa wajen tauye min haƙƙi na ’yar majalisa.”

Daga nan sai ta sauka daga kujerarta zuwa gaban Akpabio, inda ta rusuna sannan ta ajiye takardun ƙorafinta.

Shugaban Majalisar, Sanata Akpabio, ya karɓi ƙorafin, inda ya miƙa shi ga Kwamitin Ladabtarwa da Tsare-Tsare domin gudanar da bincike.

Ya ce: “Na miƙa wannan ƙorafi ga kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawa domin yin bincike kuma su dawo mana da rahoto cikin gaggawa.”

Duk da haka, yayin da ake tattaunawa, Babban Mai Tsawatarwa na Majalisa, Sanata Mohammed Monguno, ya ce ba za a iya tattauna ƙorafin ba saboda yana da nasaba da shari’ar da ke gaban kotu.

Sai dai Sanata Natasha ta musanta hakan, inda ta bayyana cewa ƙarar da ake yi a kotu ba ta shafi ƙorafin da ta gabatar ba.

Ta bayyana cewa abin da ke gaban kotu na da nasaba da wani hadimin Akpabio, Patrick Mfon, wanda ya zarge ta da sanya kayan wanda ba su dace ba a majalisar.

Martanin Sanata Akpabio

Bayan karɓar ƙorafin, Akpabio ya musanta duk wasu zarge-zarge da Natasha ta yi masa.

Ya ce: “Dangane da zargin da ake yi min, babu lokacin da na taɓa yunƙurin cin zarafin Sanata Natasha ko wata mace.

“Mahaifiyarmu ta ba mu tarbiyya tun muna ƙanana, kuma ni ma ina da ’ya’ya mata huɗu. Bugu da ƙari, lokacin da nake gwamna, an taɓa karrama ni a matsayin gwamnan da ya fi kowa girmama mata.”

Akpabio ya kuma jaddada cewa lamarin na gaban kotu, don haka ya buƙaci kafafen watsa labarai da al’ummar Najeriya su jira sakamakon shari’a.

Sanata Natasha Ba Ta Samu Goyon Bayan ’Yan Majalisa Ba

Bayan gabatar da ƙorafin, mafi yawancin ’yan majalisar dattawa da suka yi tsokaci ba su goyi bayan Natasha ba, har da sanatoci mata ’yan uwanta.

Wasu daga cikinsu sun ce ƙorafin ba shi da tushe, don haka bai kamata a tattauna shi a zauren majalisar ba.

Wasu kuma sun nemi a yi zaman sirri domin tattauna lamarin, amma Akpabio ya ƙi amincewa da hakan saboda akwai baƙo da ya ziyarci majalisar daga Birtaniya, wanda ke kallon yadda zaman majalisar ke gudana.

Daga ƙarshe, yayin da ’yan majalisar suka ci gaba da aikinsu, Sanata Natasha ta fice daga zauren majalisar domin nuna rashin jin daɗinta da yadda lamarin ya kaya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kwamiti Ƙorafi Majalisar Dattawa Zargin Cin Zarafi Shugaban Majalisar gaban Majalisar

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ya Raba Tallafin Ramadan A Mazabarsa

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Dahiru Liman, ya raba kayayyakin agaji na watan Ramadan na sama da Naira miliyan 200 ga al’ummar mazabarsa.

Ya yi hakan ne da nufin tallafa wa al’umma domin samun damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki, duba da halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki.

A wajen bikin kaddamar da rabon, Yusuf Dahiru Liman, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan ofishinsa, Bashir Adamu Nababa, ya jaddada aniyarsa ta rage wahalhalun da al’ummar mazabarsa ke fuskanta.

Ya bayyana rabon kayayyakin a matsayin wani bangare na alkawarin da ya dauka na inganta walwalar jama’a a yayin  yakin neman zabe.

Shugaban kwamitin masu ruwa da tsaki, Isiyaku Adamu Nababa, ya jaddada cewa shirin ya nuna irin sadaukarwar da shugaban majalisar yake yi na yi wa al’ummarsa hidima baya ga  ayyukan majalisa.

Ya bayyana sauran ayyukan jin kai da Yusuf Liman ya jagoranta, da suka hada da ayyuka a fannin ilimi, da  kiwon lafiya, da kuma sanin makamar aiki.

Da yake jawabi a wajen taron, Hakimin Barnawa, Alhaji Kabiru Zubairu, ya bayyana jin dadinsa bisa jajircewar da kakakin majalisar ya yi wajen kyautata rayuwar al’ummar mazabarsa.

Ya yaba da yadda shugaban majalisar ke gudanar da jagoranci, wanda ke tafiya da kowa ba tare da  bambancin addini ko kabila ba.

Shi ma mataimakin shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Nehemiah Baba Karik, ya yaba da yadda Shugaban Majalisar yake aiki ba tare da nuna son kai ba, inda ya ce yana yi wa dukkan mazauna yankin hidima bisa adalci.

A nasa jawabin,  Shugaban Majalisar Limamai da Malamai na mazabar Makera Malam Ibrahim Mahe, ya yaba da wannan karamci, inda ya ce ya zo a daidai lokacin da dace.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya sakawa shugaban majalisar bisa kokarinsa na tallafawa al’ummar jihar Kaduna.

Wadanda suka ci gajiyar wannan karimcin sun hada da malamai maza da mata na makarantun islamiyya, da manyan limamai, da  kungiyoyin Nisa’us Sunnah na Barnawa, da Makera, da Kakuri, da masu rike da  sarautun gargajiya, da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, da sauransu.

Sauran sun hada da hukumomin tsaro da suka hada da rundunar sa kai ta  Civilian JTF, da kuma kungiyoyin agaji na  JIBWIS, da  Fityanul Islam, da Jama’atu Nasril Islam da dai sauransu.

Da dama daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin sun nuna matukar godiya ga wannan karamcin, inda suka yi addu’o’in Allah ya ci gaba da yi ma shugaban majalisar jagoranci da samun nasara a ayyukansa.

 

Shamsuddeen Mannir Atiku

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwamitin Majalisa Ya Yi Watsi Da Ƙorafin Da Natasha Ta Shigar A Kan Akpabio
  • Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio
  • Natasha Da Akpabio: Sanata Natasha Ta Gabatar Wa Majalisar Dattawa Ƙorafinta
  • An Koya Min Girmama Mata – Akpabio Ya Musanta Zargin Cin Zarafin Natasha
  • Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ya Raba Tallafin Ramadan A Mazabarsa
  • Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio
  • Majalisar Dattawa Ta Ki Amincewa Da Tattaunawar Kai Tsaye Da Natasha A Gaban Kwamitin Majalisar 
  • Dalilin da ba za mu binciki Akpabio kan zargin cin zarafin Natasha ba — Majalisar Dattawa
  • Natasha-Akpabio: Ƙungiyar Mata Ta Nijeriya Ta Gabatar Da Buƙatu Huɗu