Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio
Published: 5th, March 2025 GMT
Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na Majalisar Dattawa, ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar kan Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, inda ta zarge shi da cin zarafinta.
Kwamitin ya bayyana ƙorafin a matsayin “mattacen ƙorafi tun kafin a duba shi.”
Zargin Cin Zarafi: Natasha ta gabatar wa majalisa ƙorafinta game da Akpabio Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a BauchiA ranar Laraba, kwamitin ya bayyana cewa ƙorafin bai cika ƙa’ida ba.
Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya ce Natasha ce da kanta ta sanya hannu a kan ƙorafin, maimakon wani ya sa mata hannu, wanda hakan ya sa ya zama mara inganci.
Haka kuma, ya bayyana cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin tuni suna gaban kotu, don haka majalisa ba ta da ikon yin hukunci a kansu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe Shugaban coci da wata mace a Benuwe
A wani sabon tashin hankali ya yi sanadiyyar rasa rayukan wani shugaban cocin Roman Katolika da wata mata a ƙauyen Ayua da ke gundumar Mbayer/Yandev a ƙaramar hukumar Guma a Jihar Benuwe.
Shedun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne a daren ranar Talata, lamarin da ya sa mazauna yankin da ke kewayen yankin Mbagwen da ke ƙaramar hukumar Guma ƙaurace wa gidajensu sakamakon hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa.
An sako limamin Katolika da aka sace a Kaduna An kama mutum 2 ɗauke da ƙwayar tramadol ta N150m a KanoWaɗanda aka kashen dai sun haɗa da: David Hur, shugaban shiyyar Cocin Anter Catholic da Misis Lydia Utuu ta ƙauyen Ayua.
Majiyoyi sun yi zargin cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon wata arangama tsakanin wani makiyayi da wani mazaunin ƙauyen.
Rahotanni sun ce makiyayin ya yi yunƙurin wanke kansa ne a wata hanyar ruwa ɗaya tilo da al’umma ke da shi bayan ya sha daga ciki. Wani ɗan unguwar ya nuna rashin amincewarsa, wanda hakan ya haifar da rikici inda ake zargin makiyayin ya kai masa farmaki da adda.
“Mutumin ya yi neman agaji don jawo mutanen ƙauyen zuwa wurin, amma hargitsin ya kaure da sauri zuwa wani mummunan yanayi,” kamar yadda wani mazaunin garin ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, mazauna yankin sun bar gidajensu da yawa. Har yanzu dai ana zaman ɗar-ɗar, tare da yin kira ga gwamnati da jami’an tsaro su shiga tsakani domin daƙile ci gaba da zubar da jini.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe, CSP Catherine Anene ba ta amsa tambayoyi kan lamarin ba don ƙarin haske a lokacin haɗa wannan rahoto.