Jihar Jigawa Ta Yi Garambawul Ga Dokar Bada Tallafi Ga Masu Bukata Ta Musamman
Published: 6th, March 2025 GMT
Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta yi garambawul ga dokar bada kudaden tallafi ga masu bukata ta musamman domin kara yawan kudaden tallafin daga naira dubu bakwai zuwa naira dubu goma.
Daukar wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamatin kula da al’amuran mata da cigaban al’umma na majalisar.
Da yake gabatar da rahotonsa, shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Birnin Kudu, Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim, yace kwamatin ya tattauna da masu ruwa da tsaki domin duba bukatar kara yawan kudaden da ake tallafawa masu bukata ta musamman daidai da halin da rayuwa ta ke ciki a yau.
Ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar ya hada da kara yawan makafi da kurame da kutare da sauran masu bukata ta musamman da ke amfana da wannan tallafi daga mutane 150 zuwa 200 a dukkan kananan hukumomin jihar 27.
Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim ya yi nuni da cewar, karin yawan tallafin da kuma wadanda su ke amfana na daga cikin kudurin gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta rayuwar masu rauni a cikin al’umma.
Ya bukaci dukkan masu bukata ta musamman a fadin jihar, su ci gaba da gudanar da addu’oi ga gwamnatin jihar da sauran shugabanni domin samun sukunin sauke nauyin da ke kan su tare da wanzuwar zaman lafiya da cigaban tattalin arziki da zamantakewa a Jigawa da Najeriya ba ki daya.
Bayan Akawun majalisar, Barrister Musa Aliyu Abubakar ya gudanar da karatu na 3 akan kudurin, sai shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya sanar da amincewa da kudurin ya zamo doka.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Majalisar Dokoki
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC
Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa na jihar sun sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Daga cikin jiga-jigan da suka sauya sheƙa har da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyya, da sauran masu ruwa da tsakin jam’iyyar reshen jihar.
Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a NijeriyaSanarwar ficewar ta su ta zo ne bayan kammala taron sa’o’i shida da suka gudanar a gidan gwamnatin jihar, kamar yadda sanarwar da Sanata daga jam’iyyar, James Manager, ya bayyana.
“Duk wani dan PDP na jihar har da gwamna, da tsohon gwamna Okowa, da shugaban majalisa, da shugaban jam’iyyar, da duk ciyamomin ƙanannan hukumomi mun amince mu fice mu koma APC.
“Ba zai yiwu mu ci gaba da tafiya a jirgin da zai nutsar da mu ba,” in ji Sanatan Okowa.
A nasa ɓangaren, kwamishinan yada labaran gwamnan, Aniagwu Charles, ya tabbatar da ficewar gwamnan da ma sauran jagorori da masu ruwa da tsakin PDP.