Gwamna Mallam Umar Namadi na jihar Jigawa ya karbi lasisin yin hada hadar kasuwanci na kasa da kasa, wato kasuwanci maras shinge a kan iyakar  Maigatari a hukumance, wanda hukumar kula da sarrafa kayayyaki ta Najeriya NEPZA ta bayar kwanan nan.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa manema labarai a Dutse.

Ya bayyana cewa, kwamishinan kasuwanci, da masana’antu, Alhaji Aminu Kanta ne ya mika wa Gwamna Umar Namadi lasisin a ofishinsa.

Hamisu Mohammed Gumel ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kafa wannan gwamnati mai ci ta dukufa wajen gudanar da aikin karbar lasisin aikin daga NEPZA

A cewarsa, wannan ya nuna karara da kudurin gwamnati na bunkasa tattalin arziki, da inganta harkokin kasuwanci, da kuma sanya jihar Jigawa a matsayin babbar cibiyar zuba jari da bunkasa masana’antu.

Sakataren yada labaran ya yi nuni da cewa, kafa harkar cinikayya a kan iyakar Maigatari na da nufin jawo hankalin masu zuba jari na gida da waje, da inganta samar da ayyukan yi, da bunkasa harkokin kasuwanci, musamman a yankin arewacin Najeriya.

Ya ce, Gwamna Namadi ya nuna jin dadinsa ga kokarin hadin gwiwa da ya kai ga samun lasisin tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da yanayi mai kyau don gudanar da kasuwanci yadda ya kamata.

Hamisu ya yi nuni da cewa, a karkashin gwamnatin Gwamna Umar Namadi, wannan yunkuri ya samu gagarumin ci gaba da nufin bunkasa tattalin arziki da habaka masana’antu a jihar.

Kwamishinan ya samu rakiyar Kodineta na shiyyar kasuwanci maras shinge ta Maigatari, Abdulaziz Usman Abubakar da mai kula da shiyyar Bello Abdullahi Nura.

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Lawal Ya Yaba Da Yadda Aikin Filin Jirgin Saman Zamfara Ke Tafiya

Gwamnan ya jaddada cewa yana da burin ganin an kammala waɗannan ayyuka domin amfanin al’umma, musamman hanyoyi da filin jirgin sama da ke da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziƙin jihar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Zamfara Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikata.
  • Gwamna Lawal Ya Yaba Da Yadda Aikin Filin Jirgin Saman Zamfara Ke Tafiya
  • NOA Ta Kara Daura Damarar Inganta Ayyukanta A Jihar Jigawa
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Rage Lokutan Aiki Ga Ma’aikatan Jihar
  • An Bude Taron Shekara-shekara Na Majalisar Dokokin Kasar Sin
  • Gwamnatin Libya Ta Kore Cewa Za Ta Karbi Bakuncin Falasdinawa ‘Yan Gudun Hijira
  • Angola Zata Shiga Shirin ‘Yankunan Kasuwanci’ Na Kungiyar SADC
  • Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Shirin Ciyarwar Na Watan Ramadan
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Shirin Noman Rani Na Zamani A Karamar Hukumar Maigatari