HausaTv:
2025-03-06@13:15:14 GMT

Amurka Tace A Shirye Take Ta Shiga Yaki Da China

Published: 6th, March 2025 GMT

Shugaban ma’aikatan Tsaron kasar Amurka ko Pentagon Pete Hegseth ya bayyana cewa Amurka a shirye take ta shiga yaki da China, bayan da Beijing ta tabbatar da cewa zata tunkari kasar Amurka da dukkan karfinta kan ko ta ina ta fito mana a adawar da take nunawa kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hegseth yana fadar haka a jiya Laraba a lokacinda yake hira da shirin labarai na tashar talabijin ta Foxnews na Amurka.

Seketarin tsaron tsaron ya kara da cewa dok wanda yake son zaman lafiya to ya shiryawa yaki. Don haka kasar Amurka, inji Hegseth dole ta tabbatar da tana da sojojin masu karfi da makamai masu inganci don shiriwa ko ta kwana, saboda irin yadda kasar China take samun ci gaba mai yawa a bangaren tsaron kasarta.

Yace kasar China tana son ta maye gurbin Amurka a wurare da dama a duniya. Wanda hakan barazana ce gareta.

Yace ‘muna bukatar kashe kudade wa harkokin tsaro, wadanda suka hada makamai na zamani, don ganin yankin Ido-pecific ya ci gaba da zama karkashin ikon sojojin Amurka..

Jawaban da Hegseth na zuwa ne bayan da kasar china ta bayyana anniyarta na fuskantar dukkan barazanar da Amurka zata yiwa kasar, ta kara kudin fito da kasuwanci da sauransu, duk ta inda ta fito a shirye muke mu fuskanceta.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Yemen Ta Gargadi HKI Kan Ci Gaba Da Hana Shigar Kayakin Agaji Zuwa Yankin Gaza

Ana cikin zullumi kan sake barkewan yaki a Gaza, bayan da HKI ta ci gaba da hana shigowar kayakin zuwa cikin Gaza. Sannan kungiyar Ansarull ta kasar Yemen ta yi barazanar daukar mataki a kan HKI idan ta ci gaba da hana shigar kayakin Agaji zuwa cikin gaza.

Abdullatif Al-washali wani dan siyasa a kasar ta Yemen ya bayyana cewa rufe mashigar Rafah ta inda kayakin agaji suke wucewa su shiga Gaza, wata hanya ce ta wahalarta mutanen yankin, kuma yana dai dai da cilla yaki a kan mutanen Gaza. Ya ce kasar Yemen tana iya daukar matakin soje kan HKI matukar wannan tocewar ta ci gaba.

Har’ila yau sojojiun kasar ta Yemen sun bayyana cewa inda HKI ta ci gaba da sabawa yarjeniyar da suka cimma da Falasdinawa a Gaza, sojojin suna iya daukar matakai wadanda zasu shafi cibiyoyin tsaro na HKI a cikin kasar Falasdinu da ta mamaye ko na wajen kasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Telegraph: Birtaniya Ba Ta Da Karfin Da Za Ta Rika Kada Kugen Yaki
  • Majiyar Fadar Shugaban Kasar Amurka Tace Ta Shiga Tattaunawa Kai Tsaye Da Kungiyar Hamas A Gaza
  • Lin Jian Ya Yi Bayani Kan Takardar Bayani Game Da Shawo Kan Sinadarai Masu Alaka Da Sinadarin Fentanyl Ta Sin
  • Yemen Ta Gargadi HKI Kan Ci Gaba Da Hana Shigar Kayakin Agaji Zuwa Yankin Gaza
  • An Bude Taron Shekara-shekara Na Majalisar Dokokin Kasar Sin
  • Kakaki: A Ko Da Yaushe Kasar Sin Tana Tsayawa Tare Da Kasashe Masu Tasowa
  • Za’a Gurfanar Da Mutane 40  A Gaban Kotu Kan Zargin Yin Barazana Ga Tsaron Kasa A Tunisiya.
  • OPEC Da Kawayenta Zasu Kara Yawan Man Da Suke Haka A Karon Farko Tun Shekara Ta 2022
  • CMG Zai Watsa Bikin Bude Zama Na Uku Na Majalisar CPPCC Karo Na 14