An kama korarren jami’in tsaro da ke sayar wa ’yan ta’adda makamai
Published: 6th, March 2025 GMT
’Yan sanda sun kama wani korarren jami’in shige da fice a yayin da yake kokarin sayar da makamai Ga ’yan ta’adda.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana cewa an kama jami’in ne a hanyarsa ta kai wa ’yan ta’addan bindigogi a yankin Zuma da ke Ƙaramar Hukumar Bwari.
Da yake jawabi a hedikwatar rundunar, CP Olatunji Rilwan, ya bayyana cewa dubun korarren jami’in tsaron ta cika ne a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2025.
Ya bayyana cewa jami’an rundunar yaki da masu garkuwa da mutane ƙarƙashin jagorancin OC Mustapha Muhammad ne suka kama shi, bayan samun bayanan sirri.
NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba? Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh DaurawaDisu wanda ke bayani kan ayyukan rundunar daga watan Janairu zuwa Maris na 2025, ya ce an ƙwato wasu sabbin manyan bindigogi biyu ƙirar CZ Scorpion EVO 3 A1 a hannun wanda ake zargin.
Ya bayyana cewa rundunar tana tsare da wanda ake zargin yana amsa tambayoyi
Ya kara da cewa rundunar yaƙi da masu garkuwa da mutanen ta kuma halaka wasu ’yan bindiga bakwai a wani samamen da ta kai maɓoyar ɓata-garin a ƙauyen Gidan-Dogo da Daji Kweri da ke kan iyakar Abuja da Jihar Neja.
Ya ce an kama ’yan bindiga ɗauke da bindigogi ƙirar AK47da sauran wasu makamai a yankunan.
AA cewarsa, jimillar ’yan fashi da makami 59 da masu garkuwa da mutane tara da masu kai musu bayanai 10 ne dubu su ta cika a tsawon lokacin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Tsaro Ya bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Masu Alaka
Iran Tayi Tir Da Shirin Shugaban Amurka Na Sake Tsugunar Da Al’ummar Gaza
Kakakin gwamnatin kasar iran Fatime mohajerani ta yi tir da aniyar shugaban Amurka Donald trumph na kwashe alummar gaza zuwa wasu wurare, kuma ta biyyana shi a matsayin ci gaba da siyasar kisan kare dangi kan alumma falasdinu,
Shugaban na Amurka Donald trump yayi wannan bayanin ne a taron manema labarai da yayi a fadar white hause da fira ministan isra’ila binjamin natanyaho a watan jiya, inda ya nuna aniyarsa ta kwashe alumma yankin gasa zuwa wasu kasashen larabawa. Tare da gina wajen shakatawa da babbar tashar jiragen ruwa a wajen.
Shuwagabannin kasashen laraba wa da na musulmi sun jadda mastayinsu na amincewa da yancin falasdinawa tare da yin watsi da duk wani yunkuri na rabasu da gidajensu.
Wasu masharhanta na ganin shirin na Amurka zai jawo a mata mayar da ita saniyar ware a harkokin diplomasiya har ma tsakaninta da sauran kawayenta a yankin.