An yanke wa masu fyaɗe 3 hukuncin dandanƙewa da rataya a Kaduna
Published: 6th, March 2025 GMT
An yanke wa wasu mutum uku da aka kama da laifin fyaɗe hukuncin ratayewa da kuma dandaƙewa a Jihar Kaduna.
Kwamishinar Kula da Walwalar Jama”a, Hajiya Rabi Salisu, ta bayyana fatan cewa hukuncin da kotu ta yanke wa masu laifin zai zama darasi ga masu muguwar ɗabi’ar ta fyaɗe.
Da take sanar da hakan a ranar Laraba, kwamishinar ta bayyana cewa Ma’aikatar ta yi nasara a Shari’o’i uku da ta shigar da ƙara kan masu aikata fyaɗe a shekara gudanar ta gabata.
Ta bayyana cewa daga cikin mutanen akwai wanda Mai Shari’a Nana ta Babbar Kotun jihar ta yanke masa da hukuncin dandanƙewa da kuma kisa ta hanyar rataya, a watan Yuni shekarar 2024.
An kama korarren jami’in tsaro da ke sayar wa ’yan ta’adda makamai EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700 NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba?“Ranar 6 ga watan Fabrairu, 2025 kuma Mai Shari’a B. Yusuf na Babbar Kotun Jihar Kaduna ya yanke wa na biyun hukuncin dandanƙewa da kuma kisa ta hanyar rataya kan laifin fyaɗe.
“A ranar 24 ga watan kuma Mai Shari’a Isa Aliyu in yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai fa wanda wanda aka samu da laifin.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yansanda Sun Kama ‘Yar Shekara 40 Bisa Zargin Yi Wa Almajiri Fyaɗe A Bauchi
“Yaron ya kuma ce akwai lokacin da ta ba shi wani lemun tsami da yake zaton an saka wani abu a ciki kafin abin ya faru. Ya bayyana cewa ta sha maimaita wannan aika-aikar a kansa,” Wakil ya ƙara da bayani.
Wakil ya ce a yayin bincike, wadda ake zargin ta amsa laifin da ake zarginta da shi.
Ya ce za a ci gaba da tantance bayananta, sannan a gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp