Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-03-06@13:03:33 GMT

Gwamna Zamfara Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikata.

Published: 6th, March 2025 GMT

Gwamna Zamfara Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikata.

 

Gwamna Dauda Lawal ya amince da nadin Yakubu Sani Haidar a matsayin babban shugaban ma’aikatan jihar Zamfara.

 

Nadin wanda ke fara aiki nan take, ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ta bakin babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Sulaiman Ahmad Tudu.

 

A cewar sanarwar, Haidar ya gaji Ahmad Liman, wanda ya yi ritaya a ranar 28 ga Fabrairu, 2025.

 

Haidar, wanda ya kammala karatunsa na kimiyyar siyasa a shekarar 1989 a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, an nada shi Babban Sakatare a shekarar 2012, kuma ya yi aiki a ma’aikatu da hukumomi gwamnati da dai sauransu.

 

Gwamna Lawal ya bayyana godiya ga shugaban ma’aikata mai barin gado bisa sadaukarwar da ya yi wa jihar.

 

Ya bukaci sabon shugaban ma’aikatan da aka nada da ya kiyaye mutunci tare da bin ka’idojin aikin gwamnati wajen gudanar da ayyukansa.

 

REL/AMINU DALHATU

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

NOA Ta Kara Daura Damarar Inganta Ayyukanta A Jihar Jigawa

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul  tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa.

Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan gwamnati na Dutse.

Ya jaddada cewa, hukumar za ta iya yin nasara ne kawai a jihar idan masu ruwa da tsaki kamar ofishin babban sakataren yada labaran suka hada hannu da ita.

Malam Tijjani Ibrahim ya ci gaba da bayanin cewa, makasudin ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa  tsakanin NOA da ofishin sakataren, a fannin wayar da kan jama’a game da manufofi da tsare-tsare daban-daban na gwamnatin Jihar Jigawa a dukkan matakai.

A cewarsa, a shekarar 2024, NOA ta yi kokari sosai wajen wayar da kan jama’a kan katin shaidar dan kasa da kuma tsohon taken kasa da aka sake dawo da shi.

Don haka Tijjani ya jaddada cewa akwai bukatar a kara kaimi domin ganin Najeriya ta kara samun hadin kai da wadata kasa.

Da yake mayar da martani, babban sakataren yada labarai, Hamisu Mohammed Gumel ya yabawa NOA bisa wannan ziyarar.

Ya kuma yi alkawarin ci gaba da ba da goyon baya da hadin kai don cigaban bangarorin 2.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rasha Ta Kai Hari Mahaifar Shugaban Ukraine Zelensky
  • Gwamna Lawal Ya Yaba Da Yadda Aikin Filin Jirgin Saman Zamfara Ke Tafiya
  • Ramadan: Gwamnatin Sakkwato Ta Rage Wa Ma’aikata Lokacin Aiki
  • Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ya Raba Tallafin Ramadan A Mazabarsa
  • NOA Ta Kara Daura Damarar Inganta Ayyukanta A Jihar Jigawa
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Rage Lokutan Aiki Ga Ma’aikatan Jihar
  • Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki
  • RAMADAN: Gwamnatin Jigawa Ta Rage Lokutan Aiki Ga Ma’aikatan Jihar 
  • HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja