Ayukkan Sojoji Na Taimakawa Wajen Samar da Tsaro a Taraba
Published: 6th, March 2025 GMT
Kwamandan runduna ta 6 ta sojan Nijeriya a jihar Taraba, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya karbi bakuncin mahalarta kwas din Cibiyar Bayar da Agaji ta Sojojin Najeriya (NARC) karo na 7/2025 a wani rangadin karatu a jihar Taraba a hedkwatar rundunar dake Jalingo.
A yayin ziyarar, Janar Uwa ya yi wa mahalarta taron karin haske kan ayyukan gudanar da aiki, nasarori, kalubale, da hasashen da za a yi a nan gaba, inda ya bayyana muhimman nasarorin da aka samu wajen yaki da rashin tsaro a cikin shekarar da ta gabata.
Ya yi nuni da cewa al’amuran satar mutane don neman kudin fansa, fashi da makami, da kuma rikicin kabilanci ya ragu matuka saboda jajircewar sojojin.
A wani bangare na bayanin, Janar Uwa ya baje kolin makamai da alburusai da aka kwato daga ayyuka daban-daban da aka samu nasara.
Ya yaba da kwazo da jajircewar sojojin, wanda jajircewarsu ya taimaka matuka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
A nasa jawabin, shugaban tawagar, Manjo Janar Dahiru Sanusi, wanda ya wakilci Darakta Janar na NARC, Manjo Janar Garba Ayodeji Wahab murabus, ya bayyana godiya ga kwamandan da jami’ansa bisa kyakkyawar tarba da karimcin da suka yi.
Ya yi nuni da cewa, an shirya rangadin binciken ne domin fahimtar aiki da kuma aikace-aikace na zahiri, tare da mayar da hankali musamman kan tantance tasirin ayyukan tsaro na rundunar ga kanana da matsakaitan masana’antu (SMEs) a cikin jihar.
Za a ci gaba da rangadin ne tare da ziyartan wasu muhimman wurare a fadin jihar ta Taraba, domin baiwa mahalarta damar fahimtar yanayin tsaro da kuma rawar da sojojin Najeriya ke takawa wajen samar da kwanciyar hankali da tsaro.
PR/ Sani Sulaiman
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi
Hedikwatar ’yan sandan Nijeriya ta gayyaci Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II domin amsa tambayoyi kan wani lamari da ya faru a lokacin bikin Sallah a Kano.
A baya dai rundunar ’yan sanda tare da sauran wasu jami’an tsaro a jihar sun soke duk wani hawan bikin Sallah, musamman jerin gwanon dawakai a jihar, saboda dalilan tsaro.
Motar fasinja ta kama wuta wasu sun tsallake rijiya da baya Rashin tsaro a Filato ya wuce rikicin manoma da makiyaya – MuftwangSai dai a yayin da Sarkin ke tattaki domin halartar Sallah a filin Idi na Ƙofar Mata a ranar 30 ga watan Maris, an caka wa wani ɗan banga da ke kare Sarkin wuƙa har lahira, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Bayan faruwar lamarin, wasu sun shaida wa majiyar Daily Nigerian cewa tun da farko babban Sufeton ’yan sandan ƙasar, Kayode Egbetokun ya umarci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya kama sarkin.
Kamar yadda aka samu rahoto, Kwamishinan ya bayyanawa Sufeto Janar ɗin cewa, lamarin ba shi da alaƙa da keta dokar hana hawan Sallah, kuma Sarkin bai yi amfani da dawakai wajen ziyartar gidan gwamnati ba kamar yadda al’adar ta tanada.
Sufeta Janar ya umurci sashen leƙen asiri na rundunar da ta karbe fayil ɗin ƙarar tare da gayyatar Sarkin zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.
A wata wasiƙar gayyata da ya sanya wa hannu Kwamishina ’yan sanda CP Olajide Ibitoye, sun gayyaci sarkin da ya gurfana a gaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar a ranar Talata 8 ga Afrilu da ƙarfe 10 na safe.