A wani yunkuri na bunkasa sana’o’in hannu da kuma karfafa wa masu bukata ta musamman, wata kungiya mai zaman kanta mai suna Women Farmers Advancement Network (WOFAN) ta kaddamar da wata cibiyar kasuwanci ta mata masu sarrafa kayayyaki tare da baiwa masu bukatar su 450 a yankin Karfi.

Wannan yunƙurin na da nufin ƙarfafa su 450 da kayan aikin farawa, wanda zai ba su damar yin aiki mai daraja da riba.

Da take jawabi a wajen taron, Daraktar Hukumar WOFAN-ICON2, Dakta Salamatu Garba, wadda ta samu wakilcin jami’in kula da ofishin na Kano, Alhaji Dayyabu Abubakar, ta jaddada cewa cibiyar kasuwanci za ta baiwa mata damar kula da harkokin kasuwancinsu da kuma amfani da dabarun tattaunawa da suka samu ta hanyar WOFAN.

Ta bayyana cewa, wannan shiri zai karfafawa mata ta hanyar ba su ikon sarrafa albarkatunsu, da kara samun riba, da kuma fadin albarkacin bakinsu kan batutuwan da suka shafe su.

Ta kara da cewa shirin ya yi daidai da manufofin shirin WOFAN-ICON2 a karkashin gidauniyar Mastercard, wanda ke kokarin samar da ayyukan yi mai dorewa ga matasa, mata, da masu bukata ta musanna a jihohi goma na Najeriya. Wanda shi ne shirin shekara biyar.

“Cibiyar kasuwancin Karfi ita ce irinta ta biyu a karamar hukumar Kura, bayan da aka kafa irin wannan wurin a kasuwar Kura. Kasuwar Kura, daya ce daga cikin manyan kasuwannin da dake Kano, tana sayar da hatsi sama da tireloli 500 a kullum zuwa wurare daban-daban a ciki da wajen Najeriya.”

Hakimin Karfi, Alhaji Magaji Shehu wanda Jamilu Magaji ya wakilta ya taya wadanda suka ci gajiyar shirin murna, inda ya bayyana cewa shirin ba wai kawai zai amfanar da jama’a ba, zai kuma yi tasiri ga al’umma baki daya.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Safiya Isah, Safiya Isah Kura, Rakiya Rabi’u, Haruna Sule Karfi da Sule Shehu sun nuna jin dadinsu da tallafin tare da ba da tabbacin za su yi amfani da kudaden cikin adalci.

Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, cibiyar kasuwancin ta kunshi shaguna guda uku: daya yana aiki a matsayin ofishi da mambobin kungiyar za su tattauna matsalolinsu da dabarun kasuwanci a cikin kasuwar Karfi, yayin da sauran biyun kuma aka kebe su domin gudanar da harkokin kasuwanci.

KHADIJAH ALIYU

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Karfi

এছাড়াও পড়ুন:

Wata mata ta kashe kishiyarta a Bauchi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure.

Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025.

Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700

Sai dai ya ce ’yan uwan mamaciyar suna zargi kishiyarta da hannu a mutuwarta.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Binciken farko ya kai ga kama kishiyar mamamciyar, mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28.

Da aka tambaye ta, ta amsa cewar ta shaƙe Hajara har lahira, sannan ta zuba mata ruwan zafi da ƙone gawarta don ɓoye laifinta.

Rundunar ta bayyana cewa za a ci gaba da bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID).

Hakazalika, rundunar ta ce idan buƙatar tono gawar ta taso domin yin ƙarin bincike, za ta yi hakan don tabbatar da gaskiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Za Ta Kara Ingiza Samar Da Kudaden Gudanar Da Kamfanoni Masu Zaman Kansu
  • Wata Kotu A Iran Ta Ci Taran  Gwamnatin Amurka Dala Biliyon $12.6 Saboda Haddasa Mutuwar Masu Fama Da Cutar ‘thalassemia’ A Kasar
  • Jihar Jigawa Ta Yi Garambawul Ga Dokar Bada Tallafi Ga Masu Bukata Ta Musamman
  • Majalisar Kano ta yi wa dokar hukumar tace fina-finai gyaran fuska
  • Wata mata ta kashe kishiyarta a Bauchi
  • Iran Ta Ce Dole Ne Amurka Ta Janye Mata Takunkuman Tattalin Arziki Masu Gurgurtawa Da Ta Dora Mata
  • Masar: An Kawo Karshen Taron Kasashen Larabawa Na Musamman Akan Gaza
  • Fasinjoji 16 sun ƙone ƙurmus a Ogun
  • An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a