Shugaban SWAN Ya Kafa Kwamatin Hadin Gwiwa Kan Harkar Zuba Jari
Published: 6th, March 2025 GMT
Shugaban kungiyar marubuta wasanni ta kasa SWAN, Kwamared Isaiah Benjamin, ya bukaci sabon kwamitin hadin gwiwar SWAN da aka kaddamar da su farfado da kungiyar ta hanyar jawo masu zuba jari don tallafa wa marubutan wasanni a fadin kasar nan.
Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin kwamred Isaiah Benjamin ya jaddada mahimmancin karfafa kudi ga ‘yan jaridun wasanni, yana mai baiwa kwamitin ‘yancin gudanar da aiki yadda ya kamata.
“Aikin da ke gaba yana da girma, amma ina da yakinin iya karfin ku na karfafa tattalin arzikin marubutan wasanni a Najeriya ta hanyar hadin kai. Kuna da cikakken goyon bayanmu, ”in ji shi.
Ya bayyana cewa zaben ‘yan kwamitin wanda shugaban kungiyar SWAN na jihar Nasarawa, Kwamared Smah George ya jagoranta ya dogara ne da irin nasarorin da suka samu da kuma gudunmawar da suke baiwa kungiyar.
Da yake mayar da martani a madadin kwamitin, Comrade Smah George ya nuna godiya ga hukumar zartaswa ta kasa bisa wannan dama da aka ba shi, ya kuma yi alkawarin yin aiki tukuru tare da masu ruwa da tsaki domin cika aikin kwamitin.
“Za mu bincika dukkan hanyoyin da ake da su don fitar da saka hannun jari a cikin SWAN. Ina kira ga mambobin kwamitin da su ci gaba da jajircewa kan wannan aiki domin yana da matukar muhimmanci wajen inganta walwala da kwanciyar hankali na marubutan wasanni,” inji shi.
Sabbin mambobin kwamitin da aka kaddamar sun hada da Ijeoma Peter Nwante mai wakiltar Kudu maso Gabas, Austin Ajayi arewa maso gabas, Clarkson Ogo Kudu maso Kudu, Bisi Ogunleye Kudu maso yamma, Hassan Abubakar arewa ta tsakiya da kuma Jacob Enjewo arewa maso yammat, wanda zai zama sakatare.
Aliyu Muraki/Lafia.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Lafiya nasarawa Wasanni
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamitin Tsakiyar JKS Ya Gudanar Da Taron Nazarin Tattalin Arziki
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp