Liverpool na farautar Kerkez, Real Madrid na son Konate
Published: 6th, March 2025 GMT
Liverpool na farautar ɗan wasan Bournemouth mai shekara 21 daga Hungary Milos Kerkez kan fam miliyan 40. (Telegraph – subscription required)
West Ham na kokarin ganin ta saye ɗan wasan tsakiya a Ingila, Angel Gomes mai shekara 24 daga Lille a sabuwar kaka. (Guardian)
Manchester United na tunanin ɗauko mai tsaron raga a Burnley, James Trafford mai shekara 22 ko kuma Joan Garcia mai shekara 23 daga Sifaniya, domin maye gurbin Andre Onana mai shekara 28 na Kamaru.
Real Madrid na son ɗan wasan Liverpool mai shekara 25 daga Faransa, Ibrahima Konate. (Mail – subscription required)
Real ta kuma nuna matsuwa kan ɗan wasan Bournemouth mai shekara 19 daga Sifaniya, Dean Huijsen, wanda cikin yarjejeniyarsa ake iya biyan fam miliyan 50 domin sayensa ga wata ƙungiya. (Talksport)
Barcelona na duba yiwuwar mallake ɗan wasan Newcastle mai shekara 27 daga Brazil, Bruno Guimaraes, wanda ƙungiyoyin Arsenal da Manchester City ke zawarci. (CaughtOffside)
Ɗan wasan tsakiya a Bayern Munich da Jamus, Joshua Kimmich mai shekara 30 na son zuwa Arsenal, yayinda ita ma Paris St-Germain ke nuna zawarcinta. (Bild – in German)
Ɗan wasan Manchester United da Brazil, Antony mai shekara 25, ya nuna sha’awar cigaba da zama a Real Betis idan yarjejeniyar zaman aronsa ta kawo karshe a ƙungiyar ta La Liga club. (Canal Sur, via Mail)
Liverpool ta kasance ƙungiya ta baya-bayanan da ke zawarcin ɗan wasan RB Leipzig, Benjamin Sesko mai shekara 21 daga Slovenia wanda burinsa ya je Landan, sannan Arsenal da Chelsea na bibbiyarsa. (TBR Football)
Tottenham na iya rabuwa da ɗan wasan Mali, Yves Bissouma mai shekara 28 a wannan kaka, yayinda take kokarin sake garambawul a tawagarta. (Football Insider)
West Ham ta tuntubi ɗan wasan Roma mai shekara 27 da Ingila,Tammy Abraham, da yanzu haka ke zaman aro a AC Milan. (Teamtalk)
Newcastle na duba yiwuwar saye ɗan wasan Fiorentina, mai shekara 25 daga Italiya, Moise Kean. (GiveMesport), external
Everton za ta bada damar sake daidatawa kan ɗan wasan Brazil, Richarlison mai shekara 27 daga Tottenham. (TBR Football)
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Wasanni mai shekara
এছাড়াও পড়ুন:
Wace Kungiya Ce Za Ta Lashe Kofin Zakarun Turai?
Kungiyar kwallon kafa ta PSG – wadda tuni ta lashe gasar League 1 ta Faransa na daya daga cikin kungiyoyin da ake ganin za su lashe gasar Zakarun Turai ta bana saboda karfin da tawagar take da shi sannan kuma kungiyar a gine take hadi da kwararren mai koyarwa, Luis Enrikue, tsohon kociyan Barcelona da Roma da tawagar kasar Spaniya, yana daya daga cikin kwararrun masu horarwa. Kungiyar za ta kara da Arsenal a wasan na kusa da karshe.
Wani shahararren masanin wasanni dan kasar Sifaniya, Guillem Balague na ganin PSG ce za ta lashe gasar. ”Suna da duk wani abu da ake bukata domin lashe kofin, sun iya rike kwallo, a yanzu kungiyar na da karfi, tana da masu kai hari, da na tsakiya haka ma masu tsaron baya”
Ya kara da cewa hanya guda da za a iya doke kungiyar ita ce idan ‘yan wasanta suka tare a baya domin tsare gida. ”In dai suka tsananta tsare gida to sai an cinye su, amma idan za su fito, to komai zai iya faruwa” a cewarsa.
Sai shi ma Phil McNulty, babban marubucin wasanni na BBC na ganin PSG ce za ta yi nasara a gasar. ”Suna da zaratan ‘‘yan wasa masu kai hari, misali Ousmane Dembele da Khbicha Kbaratskhelia da a yanzu ke kan ganiyarsu, ga kuma Desire Doue da Bradley Barcola wadanda matasan ‘yankwallo ne masu hazaka ”, in ji shi.
Inter Milan
Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan, kungiya ce wadda za a iya cewa babu mai kwarinta a kasar Italia domin yanayin yadda take buga wasa da yadda ba ta bari ana zura mata kwallaye a raga abu ne wanda ya kamata a kalla, sannan kuma akwai zakakuran ‘yan wasa da dama da za su taimaka wajen ganin kungiyar ta kai wasan karshe tare kuma da lashe kofin.
Shima babban wakilin sashen wasanni na BBC, Ian Dennis ya ce Zakarun na Italiya na da kwarin gwiwar lashe gasar, saboda yadda kungiyar ke da karfi musammna masu tsaron bayanta. Ya ce ”Sun fi kowace kungiya da ta rage a gasar karfin tsaron baya, kawo yanzu babu mai tsaron ragar da ya kai Yann Sommer, hana kwallo shiga raga a wasannin gasar ta bana’.
Ya kuma ce ta bangaren masu kai hari ma, kungiyar na da maciya kwallo, musamman Lautaro Martinez da a yanzu ke kan ganiyar zura kwallaye. Sannan wannan ne karo na biyu a kaka uku da kungiyar ke kai matakin wasan kusa da na karshe. Kuma kungiyar – da ke jan ragamar teburin Gasar Serie A – za ta hadu ne da Barcelona a wasan na kusa da karshe.
Arsenal
Kamar yadda kowa ya sani kungiyar Arsenal ce ta fitar da Real Madrid daga gasar a matakin kusa da na kusa da na karshe bayan doke ta 5-1 gida da waje. Wakilin sashen wasanni na BBC, Aled Howell na ganin kungiyar ce za ta lashe gasar. ”Duk da matsalolin da kungiyar ta fuskanta a bana, amma ta iya kai wa wannan mataki a gasar, ai kasan sun shirya wa gasar”, in ji shi.
”Ta fannin tsaron gida, kungiyar na da karfi sosai, haka idan ka duba ‘yan wasan gabanta hadakar Saka da Martinelli da Odegaard za su iya doke duk wata kungiya da suka ci karo da ita.
Kungiyar ta Mikel Arteta, wadda ke matsayi na biyu a teburin Gasar Premier ba ta taba lashe gasar ba a tarihi kuma ‘yan wasan kungiyar irinsu William Saliba da Bukayo Saka da Martin Ordegaard sun bayyana cewa suna son su rubuta sabon tarihi a kungiyar saboda haka za su yi iya yin su domin ganin cewa sun dauki gasar a karon farko a tarihin kungiyar.
Barcelona
Ita kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kungiya ce wadda a yanzu babu kungiyar mai sharafinta kuma ita ce ta fitar da Borussia Dortmund daga gasar. Babban wakilin sashen wasanni na BBC, Simon Stone ya ce yana ganin kungiyar ta Sifaniya ce za ta lashe gasar, saboda yadda take kara farfadowa a baya-bayan nan. ”A yanzu kungiyar ta kara karfi musamman bayanta da tsakiya da masu kai hari”, in ji Simon Stone.
Kungiyar, wadda ke matsayi na daya a gasar La Liga na da zaratan matasan ‘yan wasa da ke haskakawa a fagen kwallon kafa da suka hada da Lamine Yamal da Cubersi da Balde da Fermin da Gabi da sauransu. Sanann rabon da kungiyar ta lashe gasar tun 2015 lokacin da take da zaratan ‘yanwasa irin su Lionel Messi da Luis Suares da kuma dan wasa Neymar na Brazil.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp