HausaTv:
2025-04-05@22:31:08 GMT

Telegraph: Birtaniya Ba Ta Da Karfin Da Za Ta Rika Kada Kugen Yaki

Published: 6th, March 2025 GMT

Jaridar Telegraph da ake bugawa a Birtaniya ta buga wata kasida da a ciki ta bayyana  zancen aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya a matsayin abin dariya wanda yake son komawa da gaske bayan da ya kasance abin dariya.

Marubuciyar wannan kasida Allison Pearson ta ce ba a taba yin wani lokaci da fira ministan kasar ya zama abin dariya ba, kamar a kwanaki kadan da su ka gabata da ya mike a gaban majalisa ya yi barazanar aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya.

Haka nan kuma ta zargi Fira ministan kasar da cewa za su yi amfani da batun kara yawan taimakon soja ga Ukiraniya domin kara haraji a cikin gida.

Tun bayan da aka yi cacar baki a tsakanin shugabannin Amurka da na Ukiraniya ne dai, Donald Trump ya rattaba hannu akan dakatar da duk wani taimako na soja da kudade ga kieve, da hakan ya sa kasashen turai tunanin yadda za su cike gurbin Amurka.

Birtaniya da Faransa suna cikin na gaba-gaba wajen fito da tunanin yadda za su bai wa Ukiraniya taimakon da take da bukatuwa da shi,domin ci gaba da fada da Rasha.

Macron na Faransa ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi turai ta bar Amurka ta zama ita ce mai ayyana makomarta, kuma zama ‘yan kallo akan abinda yake faruwa a duniya,yana da hatsari matuka.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Al-Azhar ta yi kira da a kama Netanyahu a matsayin mai laifin yaki

Cibiyar da ke sa ido kan tsattsauran ra’ayi da ke karkashin cibiyar ilimi ta Al-Azhar ta Masar, ta fitar da wata sanarwa da ta yi kira da a kame firaministan Haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu a matsayin mai laifin yaki.

Shafin sawtbeirut.com ya bayar da rahoto kan sanarwar da ke cewa, cibiyar yaki da tsattsauran ra’ayi ta Al-Azhar, ta yi Allah wadai da tarbar da kasar Hungary ta yi wa firaministan Isra’ila, wanda ke fuskantar sammaci na kasa da kasa da kotun ICC ta bayar, ta kuma sanar da cewa: “Manufar wannan mataki shi ne tauye matsayin kotun kasa da kasa da kuma keta hurumin ta.”

Sanarwar ta ce: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa alama ce ta tabbatar da adalci a duniya, kuma dole ne kasashen duniya su hada kai wajen mara mata baya wajen hukunta masu aikata laifukan yaki.

Kungiyar ta bayyana cewa: shawarwarin kasa da kasa da hukunta wadanda suka aikata laifukan yaki shi ne ginshikin tabbatar da zaman lafiya da adalci, kuma mutane suna da daidaito a gaban doka, babu wani wanda yake a birbishinta.

Sanarwar ta ce: “Babu lokacin yin shiru kana bin da yake fruwa, domin yin shiru yana halasta sabbin laifuka, kuma Gaza ta kasance share fage ne kawai ga ci gaba da aiwatar da bakaken manufofi da zubar da jini, da kashe rayuka.

An fitar da wannan sanarwa ne bayan da kasar Hungary ta yi maraba da firaministan Isra’ila duk da cewa kotun kasa da kasa  ta bayar da sammacin kama shi.

A watan Nuwamba 2024, Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta ba da sammacin kama Benjamin Netanyahu bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil adama a Gaza.

Duk da wannan hukuncin, Netanyahu ya isa kasar Hungary inda ya gana da firaministan kasar Viktor Orban.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sharhin Bayan Labarai: Amurka Ba Zata Taba Zama Mai Kawo Karshin Yaki A Gaza Ba
  • Babban Mashawarcin Gwamnatin Wucin-Gadi Ta Kasar Bangladesh Ya Tattauna Da Wakiliyar CMG
  • Al-Houthi: Hare-haren Amurka sun kasa dakatar da gwagwarmayar Yeman
  • Adadin mutanen da suka mutu a girgizar kasa a Myanmar ya karu zuwa 3,354
  • Pezeshkian: Iran ba ta neman yaki da kowace kasa
  • Al-Azhar ta yi kira da a kama Netanyahu a matsayin mai laifin yaki
  • Kasar Sin Ta Sanar Da Daukar Matakan Hana Fitar Da Kayayyaki Zuwa Kasashen Waje Kan Wasu Ma’adinan Da Ba Kasafai Ake Samun Su Ba
  • Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Matakan Harajin Fito Na Amurka Sun Sa Ta Zama Makiyiyar Duniya
  • Dakarun Yemen Sun kai hari kan jirgin ruwan yaki na Amurka USS Harry Truman da makamai masu linzami
  •  Kasar Afirka Ta Kudu Tana Ci Gaba Da Bibiyar “Isra’ila” A Kotun Duniya Ta Manyan Laifuka