Allah Ya yi wa babban malamin Musulunci a Najeriya Sheikh Sa’idu Hassan Jingir rasuwa, bayan fama da rashin lafiya.
Marigayi Sheikh Sa’idu Hassan Jingir shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na II na Ƙasa Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bida Wa Iqamatis Sunan (JIBWIS).
Ana sa rana gudanar jana’izarsa da misalin ƙarfe biyu 2:00 na rana a Masallacin Santa, Unguwar Rimi cikin birnin Jos.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin APC na Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu
Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu.
Ya rasu ne a ranar Juma’a, 4 ga watan Afrilu, 2025, yayin da yake jinya a ƙasar waje kan wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.
An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a BauchiIyalansa sun tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa, inda suka bayyana shi a matsayin mutumin kirki kuma jajirtacce.
Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, wanda Oladunjoye ke yi wa aiki a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce rasuwarsa babban rashi ne.
Ya ce Oladunjoye mutum ne mai kishin jam’iyya, jajirtacce, kuma ya taka rawar gani wajen tallata APC a jihar.
Za a sanar da lokacin jana’izarsa daga baya.