Majalisar Dattawa na shirin dakatar da Natasha na wata 6
Published: 6th, March 2025 GMT
Kwamitin Majalisar Dattawa ya bayar da shawarar a dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, na tsawon watanni shida.
Kwamitin ladabtarwa da ɗa’a ne, ya bayar da shawarar biyo bayan zargin da ta yi wa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, kan cin zarafinta.
Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya rasu A yi adalci a binciken mutuwar dan kwallon Nijerirya a Uganda —Gwamnatin SakkwatoA zaman Majalisar Dattawa na ranar Alhamis, Shugaban kwamitin, Neda Imasuen, ya gabatar da rahoton kwamitin, inda ya bayyana cewa Natasha ta ƙi bayar da haɗin kai wajen binciken da aka yi.
Kwamitin ya kuma bayar da shawarar a dakatar da biyanta albashi tare da janye mata jami’an tsaron da ke kula da ita.
Rikicin ya fara ne bayan da Sanata Natasha ta zargi Akpabio da ƙin amincewa da wasu ƙudurorinta, musamman wanda ya shafi Kamfanin Ƙarafa na Ajaokuta.
Haka kuma, ta ce Akpabio ya kira ta da suna “yar kulob” a zaman Majalisar, kodayake daga baya ya ba ta haƙuri.
A martaninsa, Akpabio ya musanta dukkanin zarge-zargen, inda ya bayyana cewa yana girmama mata kuma bai aikata wani abin da bai dace ba.
Wasu Sanatoci sun samu bambancin ra’ayi game da hukuncin dakatarwar.
Sanata Abba Moro daga Benuwe ta Kudu, ya bayar da shawarar a rage wa’adin dakatarwar zuwa watanni uku kawai, yayin da wasu ke goyon bayan hukuncin watanni shida.
Yanzu Majalisar Dattawa za ta tattauna kan rahoton kwamitin domin yanke hukunci na ƙarshe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: cin zarafi dakatarwa Kwamiti Majalisar Dattawa zargi Majalisar Dattawa
এছাড়াও পড়ুন:
Nigeria: An Kafa Kwamitin Bincika Hanyoyin Kare Hatsurra Akan Doron Ruwa A Cikin Kasar
Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin sakataren kwamitin wanda dama shi ne mataimakin darakta na hanyoyin ruwa na cikin gida a wannan ma’aikata.
Ministan ma’aikatar tattalin arziki na ruwa, Adegboyega Oyetola ne ya kaddamar da kwamitin da zai yi aiki tukuru domin kare hatsurran kwale-kwale da kananan jiragen ruwa a cikin kasar.
Ministan da yake Magana a wurin kaddamar da wannan kwamitin a birnin Abuja, ya yi kira da a yi aiki tukuru domin magance yawan hatsurran da ake samu na jiragen ruwa a cikin gida wanda yake haddasa asarar rayuka da dama.
A Nigeria dai ana yawan samun hatsarin kananan jiragen ruwa masu jigilar mutane musamman ma dai a cikin arewacin kasar, da hakan yake haddasa asarar rayuka da yawa. Cunkoson mutanen da suke hawa knanan jiragen da kuma rashin rigunan tsira idan hatsari ya faru, suna cikin dalilin asarar rayuwa masu yawa da ake samu. Haka nan kuma karancin masu ceto mutane da za su zama aikinsu kenan a gabar ruwa, idan aka sami bullar hatsurra.