Jami’an NDLEA Sun Kashe Budurwa A Kano, An Damƙe Su
Published: 6th, March 2025 GMT
Jami’an hukumar yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Kano sun shiga hannu bayan sun harbe wata budurwa mai shekaru 19, Patience Samuel, a unguwar Jaba.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:55 na dare a ranar Laraba, inda rahotanni suka nuna cewa jami’an ‘yansanda sun kai ɗauki, suka kwashe ta zuwa Asibitin koyarwa na Abdullahi Wase, inda aka tabbatar da rasuwarta.
An kama jami’an biyu, Nass Ridwan Usman mai shekaru 23 da Ismaila Yakubu mai shekaru 26, waɗanda ke aiki a shalƙwatar NDLEA a Kano.
Har yanzu NDLEA ko ‘yansanda ba su fitar da wata sanarwa dangane da lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Fashewar bam a mota ta kashe mutum takwas a Borno
Wani abin takaici ya sake afkuwa a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa a Jihar Borno mai cike da tashin hankali, yayin da wani bam ya tarwatse a safiyar Asabar da rana, inda aƙalla mutane takwas ne suka mutu.
Wasu shaidun gani da ido na nuni da cewa fashewar bam ɗin da ake kyautata zaton mayaƙan Boko ne suka dasa shi ya tarwatsa wata motar bas ƙirar Toyota “Hummer Bus” da ke ɗauke da fasinjoji zuwa Maiduguri babban birnin Jihar Borno.
An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato An kama mutum 8 kan faɗan daba a KanoWata majiya mai tushe da aka zanta da ita, ta tabbatar da cewa aƙalla mutane bakwai da suka haɗa da direban motar ne ake fargabar sun mutu a wannan mummunan fashewar.
Titin Maiduguri zuwa Damboa ya kasance muhimmiyar hanyar mota da ta haɗa birnin Maiduguri zuwa ƙaramar hukumar Damboa da sauran al’ummomin kudancin Borno wadda a kullum ake fargabar bin ta lura da cewar tana gab da dajin Sambisa.
Don haka wannan lamari na baya-bayan nan ya zama babban abin tunatarwa game da barazanar tsaro da ke fuskantar matafiya da ke bin wannan hanya mai muhimmanci.
Har yanzu dai hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
To sai dai kuma babu shakka wannan harin zai ƙara dagula al’amura game da lafiyar masu tafiye-tafiye da sufuri a yankin da kuma yankin da ake da ’yan tada ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabas.