Aminiya:
2025-03-06@18:24:47 GMT

Gwamnatin Ogun ta rufe kamfanoni saboda mutuwar ma’aikata

Published: 6th, March 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Ogun ta rufe masana’antu guda biyu, na Quantum Steel Industry da ke Ogijo, a Ƙaramar Hukumar Sagamu da kuma kamfanin Xinfeng Plastics Limited da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.

An rufe kamfanonin sakamakon haɗurran da ake samu a masana’antun da suka yi sanadin asarar rayuka.

An sako ɗaliban jami’ar da aka yi garkuwa da su a Binuwai An yanke wa masu fyaɗe 3 hukuncin dandanƙewa da rataya a Kaduna

An rufe kamfanin Quantum Steels saboda fashewar wani abu da ya raunata wasu ‘yan Najeriya bakwai da ma’aikata ‘yan ƙasashen waje.

Haka kuma an rufe kamfanin Xinfeng Plastics bayan da wani ma’aikacin na’ura mai suna Ishaku Monday ya rasa ransa sakamakon wutar lantarki.

Mai baiwa gwamna shawara na musamman kan Hukumar kare muhalli ta Jihar Ogun, OGEPA wanda kuma shi ne yake riƙe da matsayin shugaban kwamitin yaƙi da muhalli na jihar, Farook Akintunde ya ce gwamnati ta ɗauki matakin rufe kamfanonin ne domin gudanar da bincike kan musabbabin aukuwar lamarin cikin gaggawa da kuma samar da mafita don daƙile afkuwar lamarin nan gaba.

“A matakin gwamnati, mun ƙuduri aniyar gudanar da sahihin bincike tare da gayyato masana harkokin tsaro na waje domin gano musabbabin faruwar wannan lamari domin kare lafiyar jama’a.

“Abin da ya fi muni shi ne, duk da ziyarar da gwamnatin jihar ke kai wa waɗannan kamfanoni a kai-a kai kamar yadda sauran jihohin ke yi don wayar da kansu kan buƙatar bin ƙa’idojin tsaro, irin waɗannan al’amura sun faru a cikin gudanar da harkokin kamfanin da suke samar da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka, don haka akwai buƙatar a rufe su,” in ji shi.

Akintunde ya ƙara da cewa kamfanonin biyu za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an kammala bincike tare da kafa sababbin ƙa’idojin tsaro.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Quantum Steel Industry

এছাড়াও পড়ুন:

PDP Ta Caccaki Gwamnan Gombe Saboda Rabon Tallafin Abinci….

Jam’iyyar PDP a jihar Gombe ta bayyana rashin jin dadin ta ga gwamna Inuwa Yahaya kan rabon kayan abinci da gwamnatin tarayya ta baiwa jihar a matsayin tallafin azumin watan Ramadan.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar Abdulkadir Ahmad ya fitar a Gombe.

 

Jam’iyyar ta caccaki gwamnatin jihar kan rashin amincewa da rawar da gwamnatin tarayya ta taka, wanda hakan ya sanya ake yaudarar jama’a wajen ganin cewa tallafin na jiha ne kawai.

 

Jam’iyyar adawa ta ba da shawarar cewa yin shiru ya sa ayar tambaya game da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da kayayyakin agaji.

 

Ta kuma yi zargin cewa sukar da Gwamnan ya yi a baya game da ayyukan da gwamnatin tarayya ta yi, gami da rabon tireloli 20 na shinkafa a shekarar da ta gabata, na nuni da wani salon mayar da kokarin gwamnatin tarayya baya tare da sanya siyasa a rarraba kayan abinci.

COV HUDU

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsarin Sufuri: Gwamnatin Kano da kamfanin Stata sun ƙulla yarjejeniya
  • Sin Za Ta Kara Ingiza Samar Da Kudaden Gudanar Da Kamfanoni Masu Zaman Kansu
  • Ayukkan Sojoji Na Taimakawa Wajen Samar da Tsaro a Taraba
  • A yi adalci a binciken mutuwar dan kwallon Nijerirya a Uganda —Gwamnatin Sakkwato
  • PDP Ta Caccaki Gwamnan Gombe Saboda Rabon Tallafin Abinci….
  • Sibil Difens za ta da ɗauki sabbin ma’aikata
  • Wata Kotu A Iran Ta Ci Taran  Gwamnatin Amurka Dala Biliyon $12.6 Saboda Haddasa Mutuwar Masu Fama Da Cutar ‘thalassemia’ A Kasar
  • Ramadan: Gwamnatin Sakkwato Ta Rage Wa Ma’aikata Lokacin Aiki
  • Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki