Idan Kunne Ya Ji, Jiki Ya Tsira
Published: 6th, March 2025 GMT
Har ila yau, jim kadan bayan ficewar Zelenskyy daga Washington, shugabannin kasashen Turai da suka hada da na Jamus da Faransa da Italiya da kuma Birtaniya suka yi gaggawar mara masa baya, yayin da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi kakkausar suka ga Ukraine wanda a cewar Sanata Lindsey Graham na jam’iyyar Republican ta South Carolina, “sanadiyyar wannan ganawar da ta bar baya da kura, ka iya kawo karshen goyon bayan Washington ga Kyiv.
Shin abin tambaya a nan, da gaske ne wannan yunkurin na Amurka don kawo karshen rikici ne a tsakanin Ukraine da Rasha ko kuwa don amfanin kanta ne? Me ya sanya gwamnatin Trump ta fara wani gangamin tonon silili mai zafi kan Zelenskyy?
Kwanakin baya sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya yi nuni da cewa, yunkurin Ukraine na shiga kungiyar NATO abu ne mara tabbas, tare da bai wa Kyiv shawarar daina fatan mallakar wani yankin kasa daga Rasha. Washington ta tattauna da Moscow a Saudi Arabia ba tare da Kyiev ba, wanda hakan ke nuna cewa za a iya yanke shawarar makomar Ukraine ba tare da saninta ba.
Bugu da kari, Trump ya kira Zelenskyy a matsayin “mai mulkin kama karya,” yana zargin Kyiv da fara tsokano rikici da Moscow. Sannan ya bukaci Zelenskyy ya rattaba hannu kan yarjejeniyar ma’adinai da Amurka da sauri, in ba haka ba, zai iya rasa duka kasarsa ga Rasha. A yayin ganawarsu ta ranar Juma’a, Trump ya zargi Zelenskyy da yunkurin kawo yakin duniya na uku. Duk wannan barazanar don cimma muradan son zuciyar Amurka na matsawa Kyiev rattaba hannu kan yarjejeniyar ma’adanai.
Wannan a fili yake, Amurka tana son dawo da kudadenta na tallafin soji da ta bai wa Ukraine na tsawon shekaru ba don neman zaman lafiyar yankin ba.
Don haka, Trump ya ki la’akari da bukatar Zelenskyy na neman tabbatar masa da tsaro sai dai matsa masa kan amincewa da yarjejeniyar hakar ma’adanan Ukraine.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran ta yi kira ga kungiyar Shanghai ta yi Allah wadai da barazanar Trump
Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya baya nan kan kasar.
A taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka gudanar a birnin Moscow a ranar Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Ravanchi, ya yi kira ga mambobin kungiyar SCO da su yi Allah wadai da kalaman da shugaban na Amurka Donald Trump ya yi a baya-bayan nan kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da ya ce yana da hadari.
Majid Takht Ravanchi ya yi kakkausar suka ga barazanar harin bam da Trump ya yi a wata hira da tashar NBC News, inda ya ce, hakan ya keta dokokin kasa da kasa, da kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya wanda ya haramta amfani da karfi karara a kan iyakokin kasa da ‘yancin kai.
Takht Ravanchi ya bayyana cewa Iran ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi Allah wadai da wannan hali da ba za a amince da shi ba tare da daukar matakan da suka dace don kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya sake jaddada matsayar kasar Iran da cewa duk wani yunkuri daga Amurka zai fuskanci mai da martani cikin gaggawa.
Ya yi kira da a fitar da sanarwar hadin gwiwa ta SCO da ke yin Allah wadai da barazanar Amurka tare da yin kira ga kwamitin sulhun da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya.