Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta yi kira da a tallafa wa Falasdinawa
Published: 6th, March 2025 GMT
Sakatare-janar na kungiyar malaman musulmi ta duniya ya yi kira ga shugabannin kasashen Larabawa da su hada kai da al’ummarsu wajen goyon bayan Falasdinawa.
Babban sakataren kungiyar malaman musulmi ta duniya Ali Muhammad Al-Salabi, ya yi kakkausar suka kan ci gaba da goyon bayan da Amurka ke yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan a matsayin taka rawa a cikin laifukan da take aikatawa kan al’ummar Palastinu.
Ya yi nuni da cewa, wannan tallafin na nuni da nuna son kai na siyasa da ke neman boye laifukan kisan kare dangi take aikatawa kan fararen hular zirin Gaza da ba su da kariya.
A cikin jawabinsa, Al-Salabi ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Larabawa da na Musulunci da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tarihi, tare da ba da goyon baya ga al’ummar Palastinu.
Babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta duniya ya jaddada cewa, alhakin ceto al’ummar Palastinu, bisa la’akari da goyon bayan da manyan kasashen duniya suke bayarwa ga gwamnatin sahyoniyawan ya rataya a wuyan gwamnatocin musulmi, da kasashen Larabawa da kuma ‘yantattun al’ummomi naduniya.
Haka nan kuma ya yi kira ga muhimman cibiyoyin Musulunci karkashin jagorancin Al-Azhar da su yi amfani da dukkan hanyoyin da ake da su na matsin lamba wajen ceto Falasdinawa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: musulmi ta duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinawa 86 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Da Su Ka Gabata
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa adadin wadanda su ka yi shahada a cikin sa’o’I 24 da su ka wuce, sun kai 86, yayin da wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 287.
Asibitocin yankin na Gaza sun karbi wannan adadin na shahidai da kuma wadanda su ka jikkata, suna karbar magani.
Ma’aikatar harkokin kiwon lafiyar ta Falasdinawa ta kara da cewa ya zuwa yanzu jumillar Falasdinawan da HKI ta kashe tun daga 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu sun haura dubu 50.
Bugu da kari a halin da ake ciki da akwai gawawwakin shahidai masu yawa da suke kwance a karkashin baraguzan gidajen da HKI ta rushe da mutane a cikinsu, da kuma wadanda ta kashe akan hanya a lokacin da suke tafiyar zuwa inda za su sami mafaka.
Yankunan da HKI ta tsananta kai wa hare-hare a yau sun hada Khan-Yunus da kuma Arewacin Rafah.