Xi Jinping Ya Ziyarci Mambobin Majalisar CPPCC
Published: 6th, March 2025 GMT
Da yammacin yau Alhamis ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, ya ziyarci mambobin taro na uku na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa wato CPPCC karo na 14 ta kasar Sin, wadanda suka zo daga kungiyar dimokuradiyya ta kasar Sin, da kungiyar raya dimokuradiyya ta kasar Sin, da kuma bangarorin ilimi.
Yayin ziyartar mambobin majalisar ta ba da shawara kan harkokin siyasa, Xi ya jadadda cewa, ya kamata a karfafa amfani da ilmi don inganta kimiyya da fasaha da kuma kwararru, ta yadda za a kafa wani yanayi na amfani da kwararru baki daya.
Bugu da kari, albarkacin bikin ranar mata ta kasa da kasa mai zuwa, a madadin kwamitin kolin JKS, Xi Jinping ya mika sakon gaisuwa da fatan alheri ga wakilai mata, da mambobi mata, da ma’aikata mata da suka halarci manyan taruka biyu, da mata na dukkan kabilu, da na dukkan sassan kasar, da ‘yan uwa mata na yankin musamman na Hong Kong, da na yankin musamman na Macao, da na yankin Taiwan, da kuma Sinawa mata dake rayuwa a kasashen waje. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ta kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Za’a yi Garambawul Kan Dokar Amfani Da Shafukan Sada Zumunta A Kasar Nijer
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bayyana aniyarta ta yin garambawul ga dokar tsarin amfani da shafukan sada zumunta irin su Whatsapp da Facebook da dai sauransu a kasar.
Ministan sadarwa na kasar Nijer sidi Mohammad Raliyu shi ne ya bayyana hakan, yana me cewa duk wani zaure na Whattsapp ko Facebook da ya kunshi mutanen 50 zuwa 100 dole ne yayi rajista a wajen hukuma don ci gaba da aikinsa.
Ministan ya ce zaurukan whattsap da Facebook na zama hanyoyin kasuwanci da kuma yaƙar gwamnatoci, wannan yasa za ta bullon da sabon shiri tare da wasu ƙasashen Afirka domin sake duba dokar da ta bada damar aiki da shafukan sada zumunta a Kasashen, domin dakile amfani da ita ta hanyar da bata dace ba.