Yadda Fadada Bude Kofar Kasar Sin Ke Haifar Da Damammaki Ga Duniya
Published: 6th, March 2025 GMT
Yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke kara samun tagomashi, masana daga sassa daban daban, na ganin hakan dama ce ta ci gaban duniya baki daya. Kamar dai yadda sakamakon wani bincike, na asusun ba da lamuni na duniya IMF ya nuna yadda bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ke shafar ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.
Duba da haka, ma iya cewa duniya za ta ci gaba da shan romon bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, yayin da kasar ke ta kara fadada manufofinta na bude kofa ga sassan duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: bunkasar tattalin arzikin
এছাড়াও পড়ুন:
Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO
Shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana damuwa kan sabon harajin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya saka kan kayayyakin da ke shiga da su ƙasar daga ƙasashen duniya.
Wannan haraji ya haɗa har da kashi 14 cikin 100 na kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga Najeriya.
Ɗalibai za su koma makaranta ranar Lahadi da Litinin – Gwamnatin Kano Kakakin APC na Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasuA cewar sanarwar da WTO ta fitar a ranar Alhamis, hukumar na nazari da bibiyar matakin domin fahimtar yadda zai shafi cinikayya da kuma ci gaban tattalin arziƙin duniya.
Okonjo-Iweala, ta ce wasu ƙasashe mambobin WTO sun nuna damuwa kan wannan lamari, inda suka buƙaci ɗaukar matakan rage illar hakan.
Harajin da Trump ya sanar ranar 2 ga watan Afrilu ya zo ne daidai lokacin da ƙasashe da dama ke ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙinsu daga tasirin rikicin Rasha da Ukraine, da kuma tasirin hauhawar farashi da ake fama da shi a duniya.
Me ƙasashe ke cewa kan sabon harajin?Ƙasashe irin su China da Turai sun nuna rashin jin daɗinsu kan harajin Trump, inda China ta mayar da martani da nata sabon harajin.
A Najeriya kuwa, masana tattalin arziƙi sun fara fargabar cewa ƙarin harajin zai ƙara tsadar kayayyaki da kuma rage damar fitar da kaya zuwa ƙasashen waje.
Ƙungiyoyin cinikayya sun fara kira ga Amurka da ta janye harajin, domin gudun jefa ƙasashe masu tasowa cikin mawuyacin hali.
Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da Amurka ke cikin yanayin siyasa mai zafi, tun bayan da Trump ya sake ɗarewa karagar mulki a karo na biyu.