Shugaban NAN:Muna Iya Ganin Basirar Sin Ta Manyan Taruka Biyu Da Take Gudanarwa Yanzu
Published: 6th, March 2025 GMT
Shugaban kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN Ali Muhammad Ali ya ce manyan taruka biyu na kasar Sin wato taron NPC da CPPCC sun zama muhimmiyar hanya ta fahimtar manufofin da gwamnatin Sin ke dauka da yadda take daidaita harkokinta da basirarta na zamanantar da al’ummar Sinawa.
Ali Muhammad ya bayyana haka ne yayin hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya kara da cewa, “Da farko mun zura ido kan nagartattun manufofin da Sin take dauka na daidaita harkokinta, wadanda tarukan biyu suka gabatar da su da sakamakon da take samu dangane da hakan a fili, manufofi kuma sun sauke nauyin dake wuyansu.
Ya kara da cewa, “Ci gaban da Sin take samu na jawo hankulan kasashen Afirka matuka a halin yanzu, saboda ya samar da damammaki masu kyau. Huldar Sin da Afirka wadda ta kara zurfafa na inganta hadin gwiwar kasashe masu tasowa da samar da saurin bunkasuwa, haka ma ya gaggauta fahimta a tsakaninsu da hadin gwiwarsu.”
A cewarsa, yana fatan tarukan biyu za su fitar da karin sakon hadin gwiwar Afirka da Sin. Ya ce, “Ba ci gaban daidaita harkokinta dake jawo hankulan kasa da kasa take samu kawai ba, har ma tana gabatar da damammaki ga duniya bisa ra’ayin bude kofa da hakuri da juna. Ina fatan kasashen Afirka za su koyi basira da dabarun Sin ta hanyar zurfafa hadin gwiwarsu, ta yadda za a daidaita harkokin duniya da wadatar da duniya baki daya.” (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yadda Fadada Bude Kofar Kasar Sin Ke Haifar Da Damammaki Ga Duniya
Yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke kara samun tagomashi, masana daga sassa daban daban, na ganin hakan dama ce ta ci gaban duniya baki daya. Kamar dai yadda sakamakon wani bincike, na asusun ba da lamuni na duniya IMF ya nuna yadda bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ke shafar ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya. Binciken ya nuna bunkasar tattalin arzikin Sin da karin kaso daya bisa dari, yake haifar da matsakaicin bunkasar tattalin arzikin sauran sassan kasa da kasa da kaso 0.3 bisa dari.
Duba da haka, ma iya cewa duniya za ta ci gaba da shan romon bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, yayin da kasar ke ta kara fadada manufofinta na bude kofa ga sassan duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp