Burin Gwamnatin Sin Na Bunkasa Gdp Da Kashi 5% A Bana Ya Bayyana Niyyarta Ta Samun Ingantaccen Ci Gaban Tattalin Arziki
Published: 6th, March 2025 GMT
Ban da wannan kuma, muhimmancin wannan adadi na bayyana a bangaren iyawa da hazikanci na dan Adam. Rahoton ayyukan gwamnati na bana ya ambaci wannan abu sau da dama, ciki har da yawan amfani da na’urori dake iya sarrafa dimbin bayanai da hazikancin koyo mai zurfi da daidaita dimbin ayyuka masu sarkakiya, da kuma iyakacin kokarin bunkasa kera motocin sabbin makamashi masu aiki da basirar dan Adam.
Wasu kafofin yada labarai na kasa da kasa na ganin cewa, bunkasar wannan fanni da Sin take samu za ta yi kwaskwarima kan yanayin kirkire-kirkire a sana’o’i daban-daban na duniya, kuma kasashen duniya za su more karin ci gaba da Sin take samu ta fuskar kimiyya da fasaha na zamani. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Dalilan Da Suka Sa Gwamnatin Tarayya Zamanantar Da Wuraren Kiwo 417
A wani labarin makamancin wannan, kimanin kananan masu kiwo 100 ne a Jihar Kwara, suka amfana da tallafin kiwon Awaki na kashin farko.
Wannan tallafi, na daga cikin dabarun gwamnatin jihar na son kara bunkasa fannin da kuma samar da kudaden shiga ga masu kiwon, domin samun riba.
A jawabinta a garin Ilorin, wajen kaddamar da kashin rabon Awakin, kashi na farko; wato a karkashin shirin jin kan iyali na L-PRES, Kwamishin Bunkasa Kiwo, Oloruntoyosi Thomas ya sanar da cewa, masu ruwa da tsaki a fannin ne, suka bayar da tallafin Awakin
Thomas ya sanar da cewa, kwalliya na biyan kudin sabulu dangane da shirin L-PRES a jihar ta Kwara.
Ta sanar da cewa, Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak, ba wai kawai yana yin wadannan abubuwa ba ne don bayar da horo a bangaren kiwo a jihar, har da ma bukatar da yake da ita ta son ganin ‘yan jihar, suna samun kudaden shiga, musamman domin inganta tattalin arzikinsu da kuma na jihar baki-daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp