Ƙin yin sulhu da ’yan bindiga na haifar da alheri – Gwamnan Zamfara
Published: 6th, March 2025 GMT
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce matsayarsa na ƙin amincewa a yi sulhu da ’yan bindiga na taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a jihar.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake karɓi baƙuncin Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hassan Bala Abubakar.
An kama ’yan Pakistan biyu da laifin yin garkuwa a Legas HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Sheikh Hassan Jingir a JosAir Marshal Abubakar, ya ziyarci jihar domin yin ta’aziyya harin bam da rundunar sojin sama ta kai wa wasu mutane bisa kuskure.
Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta canza matsayarta ba game da ƙin sasanci da miyagun mutane.
“Muna shaida wa kowa cewa ba za mu zauna da ’yan bindiga ba,” in ji shi.
“Hanyar da muka ɗauka tana haifar da sakamako mai kyau, kuma muna ganin zaman lafiya yana samuwa a Zamfara.”
Gwamnan ya kuma yaba da yadda jami’an tsaro ke hanzarin amsa kiran gaggawa a jihar.
“Ina gode wa Hafsan Sojin Sama saboda matakin gaggawa da ya ɗauka. Kafin wannan ziyarar, ya aike da manyan jami’ai domin jajanta mana.
“Wannan yana nuna ƙwazo da jajircewarsu wajen kare lafiyar mutanenmu,” in ji shi.
Hakazalika, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ana gina sabon filin jirgin sama a Zamfara, kuma ya buƙaci a gina wajen ajiye jiragen rundunar sojin sama a ciki don ɗaukar matakan gaggawa kan matsalolin tsaro.
“Muna gina filin jirgin sama a Zamfara. Da zarar an kammala, muna fatan samun wajen ajiye jiragen sojin sama a cikinsa domin hanzarta ɗaukar matakan tsaro,” a cewarsa.
Air Marshal Hassan Abubakar ya gode wa gwamnan bisa yadda ya fahimci cewar harin da sojin rundunar suka kai ba da gangan ba ne.
Ya bayyana cewa sojojin sun kai hari ne bisa bayanan sirri kan ayyukan ’yan bindiga, amma daga baya aka gano cewa wasu ’yan sa-kai sun rasa rayukansu a dalilin harin.
Ya tabbatar wa mutanen Zamfara cewa rundunar sojin sama za ta ci gaba da inganta ayyukanta domin kauce wa irin wannan kuskure a nan gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Gwamna Lawal Sakamako Mai Kyau Zamfara yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba
Dakarun Soji Operation WHIRL STROKE (OPWS), sun kashe ’yan bindiga uku a Ƙaramar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba, tare da lalata sansanoninsu da kuma ƙwato makamai.
Wannan harin ya faru ne ranar 5 ga watan Afrilu, kamar yadda kakakin rundunar, Olubodunde Oni, ya bayyana a wata sanarwa.
Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya Abin da ya sa ba ma cin naman Akuya — FulaniA cewarsa, da sojoji suka isa yankin Chibi, sai ’yan bindigar suka fara tserewa.
Amma sojojin sun bi sahunsu, suka yi musayar wuta da su, har suka kashe uku daga cikinsu, sannan suka lalata maɓoyarsu tare da ƙwato makamai masu hatsarin gaske.
Sanarwar ta kuma ce sojojin sun daɗe suna sintiri a yankin Dutsen Zaki da Achalle, inda suka tarwatsa sansanonin wasu ƙarin ’yan bindiga a baya-bayan nan.
Rundunar ta ce tana ci gaba da aiki tuƙuru domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda a faɗin Najeriya.