Aminiya:
2025-03-07@00:17:33 GMT

’Yan bindiga: Har yanzu Janar Tsiga na tsare bayan kwanaki 29

Published: 6th, March 2025 GMT

Kwanaki 29 ke nan da wasu ‘yan bindiga suka mamaye garin Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutane.

An yi garkuwa da Tsiga, wanda tsohon Darakta-Janar na Hukumar Yi Wa ƙasa hidima (NYSC) ne tare da wasu mazauna garin su tara, a wata ranar Laraba.

An kama ’yan Pakistan biyu da laifin yin garkuwa a Legas Hukumar Zaɓen Neja ta sanar da ranar zaɓen ƙananan hukumomoni

Masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalan Janar ɗin da aka sace domin neman kuɗin fansa na Naira miliyan 250m.

Wata majiya ta kusa da dangin ta shaida wa wakilinmu cewa, har yanzu ana ci gaba da tattaunawa da nufin ceto Janar ɗin sojan mai ritaya.

“Abin takaici ne yadda har yanzu Janar ɗin da sauran waɗanda suka yi garkuwa da su suna hannun waɗanda suka sace su a cikin wannan wata na Ramadan.

“Zan iya tabbatar muku da cewa ana tattaunawa, kuma addu’o’inmu na tare da shi da duk sauran waɗanda abin ya shafa da ke tsare,” in ji majiyar.

Wata majiyar kuma na kusa da dangin, ta bayyana fargabar yin magana da manema labarai, inda ta ce bisa ga bayanan da aka yi ta yaɗa jita-jita game da sace Janar ɗin, zai yi musu wuya su ce komai ga ‘yan jarida.

Sai dai ya tabbatar da wata majiya na cewa ana ci gaba da tattaunawa don ganin an sako Janar ɗin.

A halin da ake ciki, rundunar ’yan sanda a Jihar Katsina ta ce, ana ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban jami’ar tarayya da ke Dutsin-Ma da aka sace.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiƙ Aliyu, ya ce rundunar ’yan sandan tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro na ƙoƙarin kuɓutar da wandanda aka sace tare da kamo masu laifin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Janar Tsiga

এছাড়াও পড়ুন:

Ƙin yin sulhu da ’yan bindiga na haifar da alheri – Gwamnan Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce matsayarsa na ƙin amincewa a yi sulhu da ’yan bindiga na taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a jihar.

Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake karɓi baƙuncin Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hassan Bala Abubakar.

An kama ’yan Pakistan biyu da laifin yin garkuwa a Legas HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Sheikh Hassan Jingir a Jos

Air Marshal Abubakar, ya ziyarci jihar domin yin ta’aziyya harin bam da rundunar sojin sama ta kai wa wasu mutane bisa kuskure.

Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta canza matsayarta ba game da ƙin sasanci da miyagun mutane.

“Muna shaida wa kowa cewa ba za mu zauna da ’yan bindiga ba,” in ji shi.

“Hanyar da muka ɗauka tana haifar da sakamako mai kyau, kuma muna ganin zaman lafiya yana samuwa a Zamfara.”

Gwamnan ya kuma yaba da yadda jami’an tsaro ke hanzarin amsa kiran gaggawa a jihar.

“Ina gode wa Hafsan Sojin Sama saboda matakin gaggawa da ya ɗauka. Kafin wannan ziyarar, ya aike da manyan jami’ai domin jajanta mana.

“Wannan yana nuna ƙwazo da jajircewarsu wajen kare lafiyar mutanenmu,” in ji shi.

Hakazalika, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ana gina sabon filin jirgin sama a Zamfara, kuma ya buƙaci a gina wajen ajiye jiragen rundunar sojin sama a ciki don ɗaukar matakan gaggawa kan matsalolin tsaro.

“Muna gina filin jirgin sama a Zamfara. Da zarar an kammala, muna fatan samun wajen ajiye jiragen sojin sama a cikinsa domin hanzarta ɗaukar matakan tsaro,” a cewarsa.

Air Marshal Hassan Abubakar ya gode wa gwamnan bisa yadda ya fahimci cewar harin da sojin rundunar suka kai ba da gangan ba ne.

Ya bayyana cewa sojojin sun kai hari ne bisa bayanan sirri kan ayyukan ’yan bindiga, amma daga baya aka gano cewa wasu ’yan sa-kai sun rasa rayukansu a dalilin harin.

Ya tabbatar wa mutanen Zamfara cewa rundunar sojin sama za ta ci gaba da inganta ayyukanta domin kauce wa irin wannan kuskure a nan gaba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƙin yin sulhu da ’yan bindiga na haifar da alheri – Gwamnan Zamfara
  • An kama ’yan Pakistan biyu da laifin yin garkuwa a Legas
  • Idan Kunne Ya Ji, Jiki Ya Tsira
  • Ɗaliban Jami’ar Binuwe Da Aka Sace Sun Sami Ƴanci
  • Trump Ya Yi Barazanar Korar Daliban Da Ke Goyon Bayan Falasdinawa
  • ‘A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice’
  • A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya — ’Yan sanda
  • Bayan Cece-ku-ce Da Zelenskyy, Trump Ya Dakatar Da Tallafin Soji Ga Ukraine 
  • Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja