Iran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Birtaniya Na Cewa Tehran Na Barazana Ga Tsaron Kasar
Published: 7th, March 2025 GMT
Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi watsi da zarge-zargen da jami’an Birtaniya suka yi na cewa Tehran na barazana ga tsaron kasar ta Burtaniya.
A cewar jami’an Iran, Ingila na zargin Iran da wani abu da ta yi fice a kai.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya mayar da martani da kakkausan lafazi kan wannan zargi, yana mai cewa wannan maganar banza ce.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafin X, ya tunatar da cewa ita kanta kasar Birtaniya kwarariya ce wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe.
A kwanakin baya ne sakataren tsaron Burtaniya Dan Jarvis ya gabatar da shawarar a gaban majalisar dokokin kasar cewa za a kara sa ido kan gwamnatin Iran da suka hada da jami’an tsaronta da kuma dakarun kare juyin juya halin Musulunci a karkashin wani sabon tsari don dakile barazanar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane 2 Sun Yi Shahada A Wani Hari Da Jirgin Sama Maras Matuki Na HKI Ya Kai Wa Kasar Lebanon
Rahotanni da suke fitowa daga yankin ‘Sahalul-Khayam na kasar Lebanon sun ce, wasu ‘yan asalin kasar Syria su 2 sun yi shahada sanadiyyar harin da Isra’ila ta kai da jirgin sama maras matuki sa’o’i 2 da su ka wuce.
Da safiyar yau Litinin ma dai wani karamin jirigin ‘yan sahayoniya ya jefa bom akan wata mota da take tafiya a garin “Beit-Lif” a kudancin kasar da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar wanda ke cikinta.
Hare-haren da HKI take kai wa a kudancin Lebanon din dai yana a karkashin keta hurumin kasar da kuma kin aiki da kudurin MDD mail amba 1701 na tsagaita wutar yakin da aka yi a ranar 27 ga watan Nuwamba na wannan shekara ta 2025.