Araghchi Ya Tafi Saudiyya Domin Halartar Taron OIC
Published: 7th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tafi kasar Saudiyya domin halartar taron ministocin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, domin tattauna matakan da za a dauka na tinkarar shirin Amurka na tilastawa mutanen Gaza gudun hijira.
A yammacin ranar Alhamis ne Araghchi ya tashi zuwa birnin Jeddah na kasar Saudiyya inda za a gudanar da taron a yammacin ranar Juma’a, in ji ma’aikatar harkokin wajen Iran.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya ce Iran ta bukaci taron ne domin jawo hankalin kungiyar OIC, a matsayinta na babbar kungiya a duniyar musulmi, kan batun da ya shafi al’ummar musulmi da kasashen musulmi.
Shirin shugaban Amurka Donald Trump na raba Falasdinawan Gaza da kasarsu ta asali ya fuskanci tofin Allah tsine a duniya.
“Iran ne ta gabatar da bukatar taron domin martani wa shirin na Trump.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Takht Ravanji: Iran Ba Za Ta Taba Yin Tattaunawa Akan Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium Ba
Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a Iran ba, ko kuma batun makamanta masu linzami.
Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa, wadannan abubuwan biyu wato dakatar da ci gaba da tace sanadarin uranium da kuma makamai masu linzami, jan layi ne da jamhuriyar musulunci ta Iran ba za ta bari a ketara su ba ba kuma za ta bari a bude tattaunawa akansu ba.
Kwamitin da yake kula da tsaron kasa da kuma siyasar waje a majalisar shawarar musulunci ta Iran a karkashin jagorancin dan majalisar Ibrahim Ridhazi ya yi taro a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka gayyaci mataimakin ministan harkokin wajen domin jin ta bakinsa akan abubuwan da suke faruwa a tattaunawar da ake yi ba kai tsaye ba da Amurka.
Ridha’i ya fada wa ‘yan jarida cewa Takht Ravanji ya kammadar da rahoto akan yadda tattaunawar take gudana a tsakanin Amurka da Iran da kasar Oman take shiga Tsakani.
Haka nan kuma ya ce; Tace sanadarin Uranium a cikin gida wani jan layi ne da ba za a tsallake shi ba.