NAJERIYA A YAU: Falalar Buɗa-baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi
Published: 7th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yana ƙara danƙon zumunci da ƙaunar juna da albarka a tsakanin al’umma.
Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu ƙarin kusanci da shaƙuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci.
Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da iyalin su al’ada.
Shin ko mene ne matsayin buɗa-baki tare da iyali a watan Ramadana?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin alfanun da buɗa-baki tare da iyali yake da shi.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Buɗa baki iyali Ramadan shan ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon Gwamnan Oyo Olunloyo ya riga mu gidan gaskiya
Tsohon Gwamna Jihar Oyo, Omololu Olunloyo ya riga mu gidan gaskiya.
Wata sanarwa da iyalansa suka fitar ta ce ya rasu yayin da rage kwanaki tara kacal ya cika shekaru 90 a doron ƙasa.
Finafinan Kannywood da suke tashe da kuma manyan marubutansu An yi wa wata mata ƙarin jini sau 36Tsohon gwamnan wanda aka haifa a ranar 14 ga watan Afrilun 1935, ya rasu ne da misalin ƙarfe 1:40 na daren ranar 6 ga watan Afrilun 2025.
Bayanai sun ce a bayan nan ya yi ’yar taƙaitacciyar jinya da ke da alaƙa da mutanen da shekarunsu suka ja.
Olunloyo ya riƙe muƙamin Gwamnan Oyo daga ranar 1 ga watan Oktoban 1983 zuwa 31 ga watan Disamban 1983 lokacin da Janar Muhammadu Buhari ya karɓi mulki.