HausaTv:
2025-05-29@19:26:46 GMT

MDD Ta Nuna Damuwarta Da Abinda ke Faruwa A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Published: 7th, March 2025 GMT

Kakakin babban sakataren MDD ya bayyana damuwarsa kan abubuwan da suke faruwa a yankin yamma da kogin Jordan, inda sojojin HKI suke ci gaba da rusa gidaje, da bata yanyuyi da kuma dukan Faladinawa da suka hadu da su a yankin arewacin yamma da kogin na Jordan.

Tashar talabijin ta Presstva anan Tehran ya nakalto Stephane Dujarric kakakin babban sakataren MDD yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa, wakilan Majalisar a yankun sun bada rahoton yadda sojojin HKI suka kutsa a cikin sansanin yan gudun hijira na al-Arroub wanda yake cikin yankin Shuyukh al-Arrub, inda suka daki wani matsayi da kasar bindiga har suka fasa masa bakinsa suka kuma karya masa kafa.

Har’ila yau rahoton ya kara da cewa yahudawan sun tilastawa falasdinawa da dama rufe shagunasu da kuma tserewa daga yankin, bayan da suka jefa masu hayaki mai sa hawaye, kuma dauki da guba..Kamfanin dillancin labaran WAFA ta Falasdinawa ya bada irin rahoto guda a yankin. Tun bayan dakarar da yaki a Gaza sojojin yahudawan sun karfafa ayyukan soje a yankin yamma da kogin Jordan da nufin korar Falasdinwa daga yankin kwatakwata

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su

Daya daga cikin maniyyata Aikin Hajjin bana daga jihar Filato mai suna Hajiya Zainab ta mayar wa da wani dan kasar Rasha kudinsa da ta tsinta a birnin Makka na kasar Saudiyya, har kimanin Naira miliyan takwas da dubu 200.

Rahotanni sun nuna matar ta tsinci guzirin maniyyacin ne a Masallacin Harami na Makka a ranar Talata .

Ta tsinci kudin ne da yawansu ya kai Dala dubu biyar, kimanin miliyan takwas da dubu 200 a Naira, idan aka canza a kan farashin N1,648 a kan kowacce Dala daya.

Babu wanda ya tayar da bam a Abuja —Wike Kotu ta yanke wa Murja Kunya hukuncin dauri a gidan yari

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da kuma Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato, Hon. Dayyabu Dauda duk sun tabbatar da faruwar lamarin.

“Ta nuna halin dattaku, gaskiya da rikon amana ta hanyar mayar da Dala dubu biyar din da ta tsinta a masallacin harami ga mai su. Hakika ta nuna halin nagarta da tausayi,” in ji Hon Dayyabu.

A wani labarin kuma, hukumar ta NAHCON ta nuna rashin jin dadinta da yadda daya daga cikin maniyyatan jihar Zamfara ta haihu a Madina a makon nan.

Hukumar ta ce ta yi mamakinn yadda matar ta tsallake duk gwaje-gwajen da ake yi a kokarin hana masu juna biyun da suka kusa haihuwa tafiya.

Sai dai ta ce za ta yi cikakken bincike domin ta gano a ina aka samu matsalar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Da Kasashen Yankin Pasifik Sun Yi Nasarar Gudanar Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Karo Na Uku
  • Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja
  • Kungiyar ASEAN Ta Bayyana Damuwarta Da Kissan Kiyashi A gaza
  •  Fiye Da Falasdinawa 60 Ne Su Ka Yi Shahada A Jiya Laraba
  • ’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su
  • Hadin Gwiwar Sin Da Yankin Turai Na Kara Kawo Haske Ga Tattalin Arzikin Duniya
  • Falasdinwan Akalla 16 Sojojin HKI Suka Kashe A Gaza Ya Zuwa Yanzu A Yau Laraba
  • Sojojin Yahudawa sun Kashe Wani Matashi A Yankin Yamma Da Kogin  Jordan
  • Yahudawan Sahyoniyya Sun Shiga Masallacin Al-Aksa Tare Da Rakiyar Sojoji
  • Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kai Wa Yankunan Gaza Hare-hare